Lalacewar tattalin arziki: Ina tausaya ma Buhari – inji Sanatan da ya kori Dino daga majalisa

Lalacewar tattalin arziki: Ina tausaya ma Buhari – inji Sanatan da ya kori Dino daga majalisa

Sanatan da ya kori Dino Melaye daga majalisar dattawa, Smart Adeyemi ya bayyana cewa yana matukar tausayin shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda karyewar farashin man fetir.

TheCable ta ruwaito Smart ya bayyana haka ne yayin da majalisar take tafka muhawara game da sabon kasafin kudin 2020 da Buhari ya mika musu a ranar Alhamis, 28 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Kowa da ranarsa: Tubabbun yan bindiga sun kwato mutane 12 daga hannun yan bindigan Zamfara

A cewar Adeyemi, lokacin da man fetir ke da tsada a kasuwan duniya, gwamnatin lokacin ta gaza wajen karkatar da akalar tattalin arzikin Najeriya, illa satar kudaden da jami’anta ta yi.

Lalacewar tattalin arziki: Ina tausaya ma Buhari – inji Sanatan da ya kori Dino daga majalisa
Smart Hoto: The Cable
Asali: UGC

“A lokacin da muke kira ga gwamnatin baya ta karkatar da akalar tattalin arzikin kasar a lokacin da gangar mai yake $100 zuwa $150, sai suka yi biris da mu, suka sace arzikin kasar.

“Ba su gina hanyoyi ba, basu gina layin dogo ba, toh ina kudin suka je? Su waye nauyin kula da arzikin kasar ya rataya a kansu a wannan lokaci? Ina tausaya ma shugaban kasa, ina tausaya ma gwamnatin nan saboda rushewar farashin mai zuwa $22 ko $30.

“Kimanin shekaru 10 da suka gabata muna da tashoshin amsan harajin amfani da manyan tituna, amma daga bisani wancan jam’iyyar ta rushe su duka, ina ganin lokaci ya yi da ya kamata duk masu hawa motocin alfarma su fara biyan gwamnati.” Inji shi.

Kazalika Sanatan ya yi kira ga masu kudi dake zama a katafaren gidaje a cikin al’umma su fara biyan gwamnati harajin kadara don taimaka ma tattalin arzikin kasar don kada ya rushe.

A wani labari, Gwamnatin Benuwe ta sanar da shirin gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar duk kuwa da hauhawar adadin masu kamuwar da cutar Coronavirus a kasar.

The Nation ta ruwaito kwamishinan kiwon lafiya kuma sakataren kwamitin yaki da COVID-19 a jahar, Sunday Ongbagbo yace mutane 6 kacal suka kamu a jahar, kuma tuni hudu sun warke.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel