COVID-19: Boss Mustapha ya sanar da inda aka kwana a yaki da annobar

COVID-19: Boss Mustapha ya sanar da inda aka kwana a yaki da annobar

- Kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar shugaban kasa ya sanar da inda aka kwana a kan yaki da annobar

- Shugaban kwamitin, Boss Mustapha ya tabbatar da cewa har yanzu gwamnati bata fitar da takamaiman maganin cutar ba

- Mustapha ya jaddada cewa PTF za ta bai wa shugaban kasa shawara nan da sa'o'i masu zuwa

Kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar shugaban kasa ta musanta rahoton cewa gwamnatin tarayya ta lissafa wasu magungunan gargajiya da za su iya yakar annobar Coronavirus.

Gidan talabijin din Channels ta ruwaito cewa shugaban kwamitin yaki da annobar kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a yau Alhamis, 28 ga watan Mayun 2020 yayin bayani a kan inda ta kwana game da cutar coronavirus a Abuja.

Legit.ng ta gani cewa sakataren gwamnatin tarayyar ya ce PTF bata lissafo wasu magungunan gargajiya ba a matsayin maganin cutar.

Ya ce an samu mace-mace masu tarin yawa sakamakon wasu cutuka da ba annobar ba.

Ya kara da cewa za su bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarwari a kan cutar nan da sa'o'i 72 a kan hanyar shawo kan cutar.

"Ba mu lissafo wasu magungunan gargajiya ba da za su iya warkar da cutar coronavirus ba. Muna samun mace-mace masu tarin yawa da ba na cutar ba.

"PTF za ta shawarci shugaban kasa a kan abinda ya dace game da coro na da sa'o'i 72 masu zuwa," yace.

Mustapha ya kara da cewa kasar nan ta shirya tsaf don yakar annobar a karo na biyu.

KU KARANTA KUMA: Yan Boko Haram 188, yan bindiga 411 muka kashe a watan Mayu - Hedkwatar Sojin Najeriya

A martanin ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya ce PTF za ta ci gaba da duba bangaren gargajiya, kasuwanci, addinai da na al'umma don yaki da cutar.

Ya ce: "Za mu ci gaba da duba fannin gargajiya, addinai, kasuwanni da al'umma don yaki da cutar."

A gefe guda, Gwamnatin jihar Kogi ta ce babu wani mahaluki da ya kamu da cutar COVID-19 da aka fi sani da korona a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A wata sanarwa da kwamishinan Lafiya na jihar, Saka Haruna Audu, ya fitar a ranar Laraba ya ce jihar tana da kayan gwaji kuma ta yi gwaje-gwaje masu dimbin yawa kuma duk sun nuna babu mai cutar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng