Kowa da ranarsa: Tubabbun yan bindiga sun kwato mutane 12 daga hannun yan bindigan Zamfara

Kowa da ranarsa: Tubabbun yan bindiga sun kwato mutane 12 daga hannun yan bindigan Zamfara

Wasu ayarin tubabbun yan bindiga a jhar Zamfara sun ceto kimanin mutane 12 da wasu miyagun yan bindiga suka sace su, kuma tuni sun mika su hannun Yansanda.

Punch ta ruwaito kakaakin rundunar Yansandan jahar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka, ina yace a ranar 27 ga watan Mayu ne tubabbun yan bindigan suka nuna bajinta.

KU KARANTA: Gaskiya ta yi halinta: Kalli wasu masoya biyu da suka gano yan uwan jini ne su gab da aurensu

“Kwamitin zaman lafiya na jahar Zamfara tare da hadin gwiwar tubabbun yan bindiga sun ceto mutane 12 daga hannun masu garkuwa da mutane. Kimanin makonni biyu da suka gabata aka yi garkuwa da mutane.

“Amma Allah Ya kubutar da su ta hannun tubabbun yan bindiga da suka kai harin kwantan bauna kan miyagun yan bindigan da suka yi garkuwa da mutanen.” Inji shi.

Kowa da ranarsa: Tubabbun yan bindiga sun kwato mutane 12 daga hannun yan bindigan Zamfara
Gwamnan Zamfara
Asali: UGC

A jawabinsa, kwamishinan Yansanda Usman Nagogo ya ce an samu nasarar ne sakamakon alkawarin da tubabbun yan bindigan suka dauka na taimaka wajen yakar abokansu.

Don haka kwamsihinan ya jinjina ma kokarin tubabbun yan bindiga bisa amincewar da suka yi da tayin gwamnati da sauran hukumomin tsaro.

Daga karshe ya yi kira a gare su su cigaba da aikinsu yadda suka fara, sa’annan ya basu tabbacin hukumomin tsaro za su cigaba da aiki tare da su don tabbatar da zaman lafiya a jahar.

A wani labari kuma, Jami’an hukumar DSS, ta sanar da kama mutumin da ya yi garkuwa da jikan fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi, mai shekaru 3 a duniya.

Punch ta ruwaito baya ga kama mutumin, jami’an na DSS sun kubutar da yaron cikin ruwan sanyi tare da kwato kudaden fansan da iyayensa suka biya don a sake shi.

A ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu ne aka yi garkuwa da jikan a gidan Shehin dake jahar Kano. Shugaban hukumar DSS reshen jahar Kano, Muhammad Alhassan ya tabbatar da lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel