Yan Boko Haram 188, yan bindiga 411 muka kashe a watan Mayu - Hedkwatar Sojin Najeriya

Yan Boko Haram 188, yan bindiga 411 muka kashe a watan Mayu - Hedkwatar Sojin Najeriya

Akalla yan Boko Haram da kungiyar daular Islamiyya a Afrika ta yamma wato ISWAP 188 suka rasa rayukansu cikin watan Mayu kadai, bisa jawabin hukumar tsaron Najeriya.

Hakazalika dakarun Sojin sun hallaka yan bindiga 411 cikin wata daya, Legit.ng Hausa ta samu labari.

An hallaka wadannan tan ta'adda da yan bindiga ne a sassa daban-daban na kasar nan da Sojoji suka kai farmaki.

A jawabin da kakakin hedkwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar John Enenche ta saki, ya ce an ceto mata da yara 236 daga hannun yan ta'adda cikin watan Mayu.

KU KARANTA: Kalli bidiyon yadda Sojoji ke ragargazan 'yan bindiga a Zamfara

Jawabinsa yace: "Hukumar Sojojin Najeriya ta gudanar da wasu manyan hare-hare a fadin tarayya kamar yadda kuka sani. Saboda haka, ya wajaba mu bayyanawa jama'a abubuwan da suka wakana."

" Wadannan hare-hare da gamayyar Sojin kasa, na ruwa, na sama da wasu jami'an tsaro na daban suka kai sun nakasa makiyan Najeriya."

"A cikin lokacin nan na wata daya, an hallaka yan Boko Haram da ISWAP 188 kuma an jikkata da dama cikinsu da suka arce da raunuka da dama kuma da wuya su rayu."

"Dakarun Operation LAFIYA DOLE sun ceto masu faron hula - mata da yara, wadanda yan ta'addan suka sace. Adadin wadanda aka ceto cikin wata daya shine 236. Ana musu gwaje-gwaje yanzu a asibitocinmu."

"Dakarun Operation HADARIN DAJI sun wargaza yan bindiga inda suka hallaka 392 cikinsu kuma suka ragargaza mazauninsu da dukiyoyinsu a Dunya, sansnain Abu Radde, sansanin Ibrahim Mai Bai dake Jibiya, karamar hukumar Danmusa na jihar Katsina, Maikomi, Kurmin Kurain Birnin Magaji da karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara."

"A takaice, daga ranar zuwa 28 na Mayu, Sojojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram da ISWAP 188 a Arewa maso gabas, yan bindiga 392 a Arewa maso yamma da kuma yan bindiga 20 a Arewa maso tsakiya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel