Ranar 17 ga watan Yuni za a dawo gasar Firimiya ta Ingila

Ranar 17 ga watan Yuni za a dawo gasar Firimiya ta Ingila

- Kungiyoyin kwallon kafa da ke buga gasar firimiya a Ingila za su dora daga inda suka tsaya a ranar Laraba 17 ga watan Yuni

- Kungiyar Arsenal da Manchester City za su fafata wasan su na farko yayin da dawo wa.

- Za a ci gaba da buga wasanni kofa kulle ba tare da 'yan kallo ba domin dakile yaduwar cutar korona

Rahotanni sun bayyana cewa, kungiyoyin kwallon kafa da ke buga gasar firimiya a Ingila, sun kada kuri'ar dawo wa fagen fama a ranar Laraba 17 ga watan Yuni.

Kungiyar Arsenal da Manchester City za su kara da juna a wasan su na farko yayin dawowa a filin wasa na Etihad.

A rahoton da kafar watsa labarai ta Sun Sport ta ruwaito, sabon jadawalin ci gaba da gasar da aka fitar zai bai wa kungiyar Sheffield United ta Aston Villa damar kara wa da juna a wasansu na farko yayin dawo wa.

Za a buga wasanni biyu a ranar Larabar da aka dawo inda zai zamana kowace kungiya ta buga wasanni 29 kenan.

Ana sa ran za a buga wasa daya a ranar Juma'a, 19 ga watan Yuni, kafin kungiyoyin su tsunduma gada-gadan wajen take leda a karshen mako.

Ranar 17 ga watan Yuni za a dawo gasar Firimiya ta Ingila
Ranar 17 ga watan Yuni za a dawo gasar Firimiya ta Ingila
Asali: Getty Images

Rahotanni sun bayyana, mahukunta gasar firimiyar ta Ingila na ci gaba da fadi-tashi wajen ganin an karkare gasar ta bana a ranar 2 ga watan Agusta.

Akwai yiwuwar masu shirya gasar firimiyar sun kammala duk wani shiri da zai ba da damar a buga wasanni 92 da suka rage na bana a cikin kwanaki 35 kacal.

KARANTA KUMA: Wakar da ta sa Ministan Labarai, Lai Mohammed, ya ba da umarnin a kama dan jarida, Jolayemi

Tuni da an kammala gasar a watan Mayu, sai dai da ya ke kaddara ta riga fata, annobar cutar korona ta sanya dole al'amura suka sauya.

A rahoton da jaridar The Telegraph ta wallafa, a yanzu dukkanin kungiyoyin masu buga gasar firimiyar ta Ingila, za su rika buga wasanni biyu cikin kowane mako kuma ba tare da 'yan kallo ba.

A halin yanzu, wasanni 9 ne su ka rage wa galibin kungiyoyin in banda 'yan kalilan da ya rage masu wasanni goma.

Hakazalika, an kammala duk wani shiri na watsa wasannin a Gidajen Talbijin domin bai wa masoya kwallon kafa damar nishadantar da kawunansu su na zaune a gida, a yayin da annobar korona ta hana su ziyarci filayen wasanni domin kallo 'ra'ayal aini'

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng