Kalli bidiyon yadda Sojoji ke ragargazan 'yan bindiga a Zamfara

Kalli bidiyon yadda Sojoji ke ragargazan 'yan bindiga a Zamfara

Hedkwatar tsaro ta ce dakarun sojin samanta na rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaza ma'adanar makamai tare da kashe a kalla 'yan bindiga 30 a samamen da ta kai ta jiragen yaki.

Dakarun sun kai samamen ne a ranar Talata zuwa dajin Doumborou da ke jihar Zamfara.

John Enenche, shugaban fannin yada labarai na rundunar, a wata takarda da ya fitar ya ce, rundunar ta kai harin ne bayan bayanan sirri da ta samu.

Bayanan sun nuna cewa akwai wata ginin jinka da ke dajin wacce 'yan bindigar ke amfani da ita wajen adana makamai.

"Babu bata lokaci aka tura jirgin yaki wanda ya gano wasu daga cikin 'yan bindigar na shawagi a babura. An bibiyesu har zuwa ma'adanar makaman inda suka ajiye wasu kayayyaki," takardar tace.

"A take jiragen yakin suka kai wa yankin farmaki tare da yin nasarar lalata ma'adanar inda ta tashi da wuta.

"Bayan nan, jirgin yakin ya bibiyi 'yan bindigar da suka fara tserewa tare da halaka 30 daga ciki," takardar ta kara da cewa.

"Shugaban rundunar dakarun sojin sama na rundunar Operation Hadarin Daji ya jinjinawa dakarun a kan kwazonsu.

"Ya umarcesu da su ci gaba da jajircewa tare da bada tallafi ta sama ga dakarun da ke kasa don kawo karshen wanzuwar 'yan bindigar. Hakan zai tabbatar da dawowar zaman lafiya yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya a kasar nan," ta kara da cewa.

Rundunar sojin Najeriyar na ci gaba da samun manyan nasarori a yayin yaki da 'yan bindiga da mayakan ta'addanci na Boko Haram.

DUBA WANNAN: Kungiya ta siya wa gwamnan APC fom din takara

A wani labari na daban, wata kungiya ta magoya bayan gwamnan Edo, Godwin Obaseki mai suna 'The Obaseki Mandate Forum' ta siya masa fom din takarar zaben fidda gwani na kujerar gwamna a jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC).

A yayin taron manema labarai da ta kira a ranar Laraba, Nathaniel Momoh, shugaban kungiyar ya ce kungiyar ta gamsu da irin kamun ludayin gwamnan ne kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel