Ranar 8 ga watan Yuni: Gwamnatin Gombe ta yi gargadi a kan bude makarantu

Ranar 8 ga watan Yuni: Gwamnatin Gombe ta yi gargadi a kan bude makarantu

Gwamnatin jihar Gombe ta bukaci a yi watsi da jita-jitar da ake yadawa kan batun komawa makarantu a ranar 8 ga watan Yuni.

Gwamnatin jihar ta bukaci hakan ne a yayin da ake ci gaba da yada jita-jitar cewa, Gwamnatin Tarayya ta kayyade ranar Litinin ta makon jibi a matsayin ranar bude makarantu a fadin kasar.

Kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito, Gwamnatin Gombe ta yi gargadi a kan bude makarantu a wannan rana da ake faman yada jita-jita.

Wannan gargadi ya fito ne daga bakin Dr Habu Dahiru, kwamishinan ilimi na jihar, wanda ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) a birnin Gombe.

Kwamishinan ya ce har yanzu ma'aikatar ilimi a jihar ba ta samu wata sanarwa ba daga Mahukuntan Gwamnatin Tarayya da suka dace sun ambaci ranar bude makarantu a fadin kasar.

Dahiru ya ce "matakin da aka dauka na rufe makarantu a fadin kasar nan manufa ce da dalibai za su ribata domin kiyaye lafiyarsu."

Gwamnan jihar Gombe; Inuwa Yahaya
Gwamnan jihar Gombe; Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

A cewarsa, "babu wata gwamnati wadda ta san ya kamata da za ta jefa yara da daliban cikin hadarin kamuwa da wannan cutar kuma muna sa ran iyaye da duk masu ruwa da tsaki za su fahimta kuma su kara hakuri."

"Ba da ra'ayin kanmu muka rufe makarantu ba. Umarni ne kawai muke bi na matakan ta Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) da Cibiyar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) suka shimfida."

"Wannan umarni ne da ya samo asali daga mahukuntan da suka dace, idan za mu sake bude makarantu sai mun samu wani sabon umarni daga gare su yayin da suka tabbatar da aminci a kan hakan."

Kwamishinan ya kara da cewa, ba su da wani shiri na sake bude makarantu a jihar har sai an tabbatar da babu hatsarin kamuwa da cutar korona.

KARANTA KUMA: Jihohi 36 da aka samu bullar cutar korona a Najeriya - NCDC

"Gabanin a sake bude makarantu, sai an yi wa makarantu feshi tare da tabbatar da sun tsarkaka daga kwayoyin cutar korona."

"Haka zalika za a wayar da kan malamai da kuma dalibai a kan hanyoyin da matakan kare kai daga harbin cutar."

Yayin jaddada hukuncin da za a dauka kan duk makarantar da ta saba doka, ya shawarci makarantu masu zaman kansu da su tabbatar sun kiyaye matakan da Mahukuntan da suka dace suka tanada domin ba wa dalibai kariya.

Ya bukaci iyaye da su tallafawa gwamnati wajen tabbatar da tsaron lafiyar dukkan yara da dalibai a jihar.

Daga karshe kuma ya ba da tabbaci a kan yadda gwamnan jihar, Inuwa Yahaha, ya sadaukar da kai domin tabbatar da tsaron lafiyar al'umma.

Idan ba a manta ba, biyo bayan barkewar annobar korona a Najeriya, gwamnatin tarayya cikin gaggawa ta ba da umarnin rufe duk wasu makarantu a fadin kasar.

Cikin sanarwar da ma'aikatar ilimi ta fitar zuwa dukkanin hukumomin ilimi na kasar, ta nemi daliban makarantu a kowane mataki da su yi zaman dirshan a gida har sai an ga abin da hali ya yi game da annobar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel