COVID-19: Cutar Korona ta bulla jihar Kogi a karon farko

COVID-19: Cutar Korona ta bulla jihar Kogi a karon farko

Watanni uku cif bayan bullar cutar korona a Najeriya, ranar 27 ga watan Mayu ya zama ranar da aka samu masu cutar mafi yawa.

Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC), ta bayyana cewa mutum 389 ne suka kamu da muguwar cutar a ranar Laraba.

A ranar ne kuma aka gano kamuwar mutum biyu a jihar Kogi bayan tsananin artabun da aka dinga da gwamnatin jihar, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Jihar Kaduna ta sake tsawaita dokar hana zirga-zirga (Bidiyo)

Duk da hauhawan yawan masu cutar korona a kasar nan, gwamnatin tarayya ta yi kira ga wasu jihohi da su samar da cibiyoyin killacewa da bada maganin cutar.

A yayin jawabi ga kwamitin yaki da cutar korona na kasa a ranar Laraba, karamin ministan lafiya na tarayya, Olorunnimbe Mamora ya ce jihohi da yawa basu shirya wa cutar ba don basu da yawan gadajen da suka kamata.

Ministan yace, "Duk da cewa ba abun mamaki bane, mun yi matukar damuwa da yadda masu cutar ke kara yawa.

"Akwai yuwuwar yawan masu cutar su wuce yadda ake tsammani tare da wuce yadda Najeriya za ta iya kula da su.

"A halin yanzu, akwai cibiyar shan maganin cutar har 112 a jihohi 36 na fadin kasar nan har da babban birnin tarayya. Akwai gadaje 5,324 na marasa lafiya..

"Yayin da jihohi biyar tare da birnin tarayya kadai suka mallaki sama da gadaje 300, wasu jihohi kuwa suna da kasa da gadaje 100 a cibiyoyin killacewarsu."

Ya kara da cewa, "A yayin da ake samun hauhawar yawan masu cutar, akwai bukatar gaggauta kara yawan cibiyoyin killacewa na kasar nan.

"A don haka nake kira ga gwamnonin jihohi da masu hannu da shuni da su tashi tsaye wajen shawo kan wannan kalubale da ke gabanmu."

A wani labari na daban, gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta musanta rade-radin da ake yi na cewa ta yi watsi da kayan tallafin da gwamnatin tarayya ta ba jihar har ruwan sama ya lalata.

Kamar yadda kwamishinan watsa labarai na jihar, Muhammad Garba, ya aika wa manema labarai a yau Talata, ya ce ba gaskiya bane zargin. Ya ce kayan na nan babu abinda ya lalace sakamakon dukan ruwan saman.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel