Yanzu-yanzu: Daga yanzu mun haramta Almajiranci a Kano - Ganduje

Yanzu-yanzu: Daga yanzu mun haramta Almajiranci a Kano - Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta haramta Almajiranci a jiharta kuma ta lashi takobin cewa duk mahaifin da ya tura dansa Almajirci zai gurfana gaban kotu.

A cewar The Sun, Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya alanta akan ne ranar Laraba yayinda yake hira da manema labarai a gidan gwamnatin jihar.

Amma dai, gwamnan ya gindaya sharruda da ya wajaba a cika ga duk wanda ke son tara yara don karatun Allo.

Ganduje ya jaddada cewa wajibi ne manhajin karatun ya hada da ilimin Boko kuma wajibi ne malami ya tanadi azuzuwa, wuraren kwana, da isasshen abinci saboda kada yaran su fita bara.

Yace: "Gwamnatin jihar ba zata lamunci Almajiranci a jihar ba. Wajibi ne yara su kasance a makaranta."

"Wajibi ne makarantar ta bi ka'idojin makaratun Boko; wajibi ne a samu kwararrun malamai, a rika rubuta jarabawa, da kuma bibiya."

"Muna tabbatarwa al'ummar jihar cewa ana karantar da ilimin addini a makarantunmu na Boko kuma muna daukan kwararrun Malamai."

Ya kara da cewa kada hankalin Malaman makarantun Allo ya tashi saboda ba wai ana kokarin kwace musu aiki bane, gwamnatin jihar na shirye da daukansu aiki sashen ilimin jihar.

Yanzu-yanzu: Daga yanzu mun haramta Almajiranci a Kano - Ganduje
Ganduje
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kungiyar Kwadago ta ba wa Ganduje kwanaki 14 ya dawo wa da ma'aikatan Kano albashinsu da ya zaftare

A bangare guda, shugaban shirin Almajiranci a jihar, Alhaji Sule Garo, ya ce kawo yanzu gwamnatin jihar ta fitar da Almajirai 1,172 zuwa jihohinsu na asali.

Ya ce an tura 419 jihar Katsina, 584 jihar Jigawa, 155 jihar Kaduna, 38 jihar Bauchi, sannan 36 jihar Gombe.

Garo ya kara da cewa jihar ta karbi bakuncin Almajirai kimanin 1000 daga sassan Arewa daban-daban.

179 daga jihar Adamawa, 220 daga jihar Nasarawa, 96 daga jihar Gombe, 18 daga Katsina, da 82 daga jihar Kaduna, kuma an killacesu na tsawon makonni biyu.

Ya ce kawo yanzu, 733 cikin wadanda aka killace tuni an mayar da su wajen iyayensu.

"Jami'an kiwon lafiyanmu sun gwada dukkan Almajiran kuma yawancinsu basu da cutar. Wadanda ke dauke da cutar an tafi da su cibiyar killacewa." Yace

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel