Jami’an DSS sun kama mutumin da ya yi garkuwa da dan gidan Dahiru Bauchi
Jami’an hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta sanar da kama mutumin da ya yi garkuwa da jikan fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi, mai shekaru 3 a duniya.
Punch ta ruwaito baya ga kama mutumin, jami’an na DSS sun kubutar da yaron cikin ruwan sanyi tare da kwato kudaden fansan da iyayensa suka biya don a sake shi.
KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya gayyaci duk almajiran da aka fatattaka daga jahohin Arewa
A ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu aka yi garkuwa da yaron a gidan Shehin dake jahar Kano. Shugaban hukumar DSS reshen jahar Kano, Muhammad Alhassan ya tabbatar da lamarin.
Muhammad Alhassan ya bayyana cewa sun samu nasarar kama mutumin ne tare da hadin gwiwar hukumar Yansandan jahar Kano.
“Mun samu nasarar cafko wanda ake zargi da aikata laifin ne ta hanyar hadin gwiwa wajen musayar bayanan sirri a Kano. Da fari mutumin dan shekara 27 mai suna Umar Ahmad ya nemi a bashi N10m kudin fansa.
“Daga bisani ya rage zuwa miliyan 6, nan da nan muka shiga bin sawunsa har muka gano mabuyarsa a daki na 27 na Hotel din Liberty a cikin titin Aba Road na unguwar Sabon Gari, jahar Kano.
“Bayan mun far ma otal din, sai muka kubutar da yaron, wanda a yanzu haka yana cikin koshin lafiya, muka kama mutumin da ya yi garkuwa da shi, sa’annan muka kwato kudaden da aka biya shi, ta hanyar kwashe su daga asusun bankinsa.” Inji shi.
Daga karshe Alhassan yace za su mika mutumin ga Yansanda don su gurfanar da shi gaban kotu.
A wani labari, Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ebonyi ta Arewa maso yamma, Victor Aleke ya yi rashin dan uwansa, kaninsa na jini a wani yanayin mutuwa mai daukan hankali.
An tsinci gawar mamacin mai suna Samuel Aleke ne a cikin sashin ajiyen kaya, watau ‘boot’ din motarsa a kan babbar hanyar Abakaliki zuwa Afikpo na jahar Ebonyi.
Rahotanni sun bayyana mamacin ya fita gida ne a ranar Asabar 23 ga watan Mayu da yamma, amma daga nan ba’a sake jin duriyarsa ba, har sai washe gari da aka tsinci gawarsa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Asali: Legit.ng