Gwamnan Zamfara ya gayyaci duk almajiran da aka fatattaka daga jahohin Arewa
Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle na maraba da duk almajiran da aka fatattaka daga jahohin Arewa su koma jaharsa, sa’annan ya dakatar da batun hana almajiranci gaba daya.
Premium Times ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Yusuf Idris cikin wata sanarwa da ya fitar, inda yace gwamnatinsa ba zata kori almajirai ba.
KU KARANTA: Kasafin kudi: Yan majalisa sun katse hutunsu na Sallah, sun koma majalisa cikin gaggawa
Tun bayan barkewar cutar Coronavirus ne gwamnoni suka fara fatattakar almajirai daga jahohinsu, a wani mataki na kare su daga cutar, da kawo karshen tsarin almajiranci gaba daya.
A yanzu haka gwamnonin jahohin Arewacin Najeriya na nazari game da tsarin da ya kamata su dabbaka wajen kawo karshen almajiranci a yankin.
Sai dai a jawabinsa, Gwamna Matawalle yace: “Gwamnati na ba za ta kori almajirai zuwa jahohinsu na asali ba, duk wadanda aka kora daga sauran jahohi ma muna maraba da su, su dawo Zamfara, zamu kula da su.”
Matawalle ya sauya ra’ayinsa ne bayan wata ganawa da yayi da manyan malamai guda 3; Abdullahi Dallah-Dallah, limamin Masallacin Dan Ashafa da kuma Sheikh Bello Kanwa.
Jim kadan bayan ganawa da wadannan Malamai ne sai gwamnan ya sanar da soke kwamitin da ya kafa na hana almajiranci a jahar.
“Mun yanke shawarar ne bayan nazarin almajiranci a jahar, tare da bukatar hada shi da tsarin karatun zamani na boko don samar ma almajirai ingantaccen ilimin zamani da na addini.
“Mun fasa fatattakar almajiran ne don nuna musu ana tare, su ma mutane ne, tare da rage kyamar da ake nuna ma karatun almajiranci a kasar nan. Almajirai na da daman samun ingantaccen ilimi a kowanne mataki a kasar.” Inji shi.
Daga karshe gwamnan yace a yanzu ya dukufa don samar da sahihin tsari da zai hada karatun almajirci da na boko a jahar ta yadda zai amfani almajiran, ba wai sallamar su daga jahar ba.
Su ma a nasu jawabin, Sheikh Dallah-Dallah da Sheikh Kanwa sun jinjina ma gwamnan bisa matakin daya dauka, kuma sun yi kira a gare shi ya gudanar da mulki na adalci.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng