Kakarsa ta yanke saka: Real Madrid da Zidane na neman dan kwallon Najeriya ido rufe

Kakarsa ta yanke saka: Real Madrid da Zidane na neman dan kwallon Najeriya ido rufe

Rahotanni sun nuna cewa mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya nuna sha’awar sayo dan kwallon Najeriya, Wilfred Ndidi don kara ma kungiyar karfi.

An ruwaito Zidane na matukar sha’awar kwallon Ndidi, don haka yake ganin shi ne kadai dan kwallon da zai iya maye gurbin Casemiero wajen rike tsakiyar kungiyar Real Madrid.

KU KARANTA: Kasafin kudi: Yan majalisa sun katse hutunsu na Sallah, sun koma majalisa cikin gaggawa

A yanzu haka kungiyoyi da dama na zawarcin Ndidi dan shekara 23, tun daga kungiyar PSG, Arsenal, Barcelona da kungiyar Manchester United, kamar yadda Real Madrid ne zawarcinsa.

Shafin cinikayyar yan wasan kwallon kafa ta kasar Spaniya mai suna fichajes.com ta bayyana cewa Zidane ya bayar da muhimmanci sosai wajen sayo Ndidi.

Kakarsa ta yanke saka: Real Madrid da Zidane na neman dan kwallon Najeriya ido rufe
Ndidi Hoto: Gettyimage
Asali: UGC

“Dan kwallon Afirkan mai wasa a tsakiya na daga cikin wadanda ake sa ran kungiyar Real Madrid za ta sayo a karshen kakar kwallon bana, kwantiraginsa a kungiyar Leicester City ya kai 2024, amma kungiyoyi da dama sun fara zawarcinsa.

“Real Madrid ta bada himma wajen ganin ta dauko dan wasan nan saboda a yanzu basu da wani dan wasan tsakiya da ya wuce Casemiro dan kasar Brazil tun bayan tafiyar Marco Llorente kungiyar Atletico Madrid.

“A halin da ake ciki, akwai yan wasa da dama da ake tunanin kungiyar na nema don cike gibin, amma wanda aka fi ambata shi ne Wilfred Ndidi, a shekarar 2016 ya tafi Leicester City daga Genk a kan kudi Euro miliyan 17.” Inji ta.

Ndidi na taka rawar gani a Leicester tun bayan zuwansa kungiyar, inda zuwa yanzu ya buga wasanni 111.

A wani labari kuma, Jagoran kungiyar Super Eagles, Ahmed Musa ya bayyana dalilin da yasa bai cika samun isashshen lokacin da yake taka leda a tsohuwar kungiyarsa ta Leicester City ba.

Musa ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da Carol Tshabalala a dandalin sadarwar zamani na Instagram, inda yace Riyad Mahrez ne dalilin lalacewar kwallonsa.

A watan Yulin shekarar 2016 ne Ahmed Musa ya tashi daga kungiyar CSKA Moscow na kasar Rasha ya koma Leicester ta kasar Ingila akan kudi pam miliyan 16.6.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel