Hasashen halin da Buhari zai shiga bayan cutar korona - Garba Shehu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bayyana a matsayin sadaukin nahiyar Afrika bayan kare yaki da annobar Coronavirus, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya yi hasashe.
A wata tattaunawa da Shehu ya yi da jaridar Daily Trust, ya ce bayan wannan annobar, ba kasar nan kadai za ta yaba wa Shugaba Buhari ba, har da kasashen Afrika sai sun jinjina masa.
Shehu yace, "Zan kare tattaunawar nan da hasashe. A yayin da wannan annobar ta tafi, za a bayyana shugaban kasar mu a matsayin sadauki kuma gwarzon COVID-19 ba a Najeriya ba kadai, har da yankin Afrika ta yamma wacce yake jagoranta."
A yayin danganta datsewar shugabanci da korona ta jawo a Najeriya, ya ce, "Wannan ba gaskiya bane. Ana ci gaba da aiki tukuru a bangaren shugaban kasa, mataimakinsa, ministoci da kowa.
"Mun mayar da hankali wajen yakar annobar amma muna ci gaba da mulki tamkar yadda yake tafiya kafin annobar.
"A watanni biyu da suka gabata, ana ci gaba da gudanar da shirin tallafin gwamnatin tarayya, majalisar zartarwa ta tarayya da sauran al'amuran mulkin kasar nan."
KU KARANTA KUMA: A karon farko: Jam'iyyar PDP ta jinjinawa Buhari a kan kokarin samar da tsaro
A gefe guda, fadar shugaban kasa ta maida martani ga rahotannin da ke kokarin nuna cewa Muhammadu Buhari ya mika ragamar mulkinsa ga marigayi Malam Abba Kyari.
A wani jawabi da babban hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya yi, ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ne wanda jama’a su ka zaba, kuma shi ne mai wuka da nama.
Garba Shehu ya karyata rade-radin da ake ji na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni a soke duk wasu mukamai da Abba Kyari ya bada daf da zai kwanta jinya.
Shehu ya na mai watsi da wadannan labarai a ranar Talata, 26 ga watan Mayu, 2020, ya ce: “Ba abin mamaki ba ne, ba a kama sunan kowa a matsayin majiyar wannan labari ba”
Mai magana da yawun bakin shugaba Buhari ya cigaba da cewa: “Babu daidai da kwayar gaskiya a cikin wadannan rahotanni, kuma ‘Yan Najeriya su yi da abin da ake nema.”
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng