Kano: Dangote bai gama gina Dakin kwantar da masu cutar COVID-19 ba

Kano: Dangote bai gama gina Dakin kwantar da masu cutar COVID-19 ba

Fiye da wata guda kenan da gidauniyar Dangote ta bada sanarwar za ta gina dakin jinya da zai ci mutane 300 masu fama da cutar COVID-19. Har yanzu ba a kammala wannan aiki ba.

Jaridar Daily Trust ta ce har zuwa ranar Talata, 26 ga watan Mayu, 2020, wannan gini bai shiga hannun gwamnatin jihar Kano domin fara kwantar da wadanda su ka kamu da cutar ba.

A jiya ranar Talatar akwai mutane 919 da aka tabbatar da cewa cutar COVID-19 ta harbesu. Bayan haka kuma wannan annoba ta kashe mutum kusan 40 da ake da labarinsu a fadin jihar.

Mai magana da yawun bakin ma’aikatar kiwon lafiya ta Kano, Hadiza Namadi, ta tabbatarwa ‘yan jarida cewa ana cigaba da aikin gina dakin, amma ba a kai ga fara kwantarwa ba tukun.

Hamshakin attajirin nan Alhaji Aliko Dangote wanda ya fito daga jihar Kano ne ya yi alkawarin gina katafaren dakin a matsayin gudumuwarsa na yaki da cutar COVID-19 a mahaifarsa.

KU KARANTA: Abin da ya sa dankin jinyar Kano bai fara aiki ba - Kwamishina

Kano: Dangote bai gama gina Dakin kwantar da masu cutar COVID-19 ba
Mai kudin Afrika Aliko Dangote
Asali: UGC

Jaridar ta ce kayan aikin ginin sun shigo Kano tun cikin watan jiya na Afrilun, kuma tun a lokacin aka fara aikin gina wannan dakin jinya a cikin filin wasan Sani Abacha a Kofar Mata.

Rahotanni sun bayyana cewa yayin da ake neman ganin karshen watan Mayu, wannan gini da ake yi a birnin na Kano bai kammala ba, hakan ya na nufin dakin jinyar bai kai ga fara aiki ba.

Kwanaki uku da su ka wuce wani Bawan Allah ya tashi zuwa filin wasan na Sani Abacha ya dauki bidiyo domin ya nunawa Duniya cewa an ci tsawon lokaci ba a iya daga ginin ba har yau.

Jaridar ta samu labari daga majiya mai karfi cewa rumfuna uku kacal aka tada a cikin babban filin wasan na Sani Abacha. Kuma babu wani maras lafiya ko mutum guda da ke kwance.

Wannan bidiyo da aka dauka aka wallafa a shafin Instagram bai yi wa gwamnatin jihar Kano dadi ba. Gwamnatin ta fito ta yi karin-haske, ta kuma bayyana inda marasa lafiyan su ke jinya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel