An cafke 'yan fashi 2 masu kwacen keke napep a Anambra

An cafke 'yan fashi 2 masu kwacen keke napep a Anambra

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Anambra, ta samu nasarar cafke wasu miyagun mutane biyu da ake zargin su da aikata laifin fashi da makami.

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, wani matukin keke napep, Joseph Asogwa, a ranar Talata ya fada tarkon 'yan fashi da makami a kan hanyar Onitsha zuwa Owerri a da ke yankin Oba na jihar Anambra.

Miyagun biyu bayan kwatar abin neman abincin na Joseph, sun kuma kwarara masa wani tafasasshen ruwa mai radadin gaske, wanda ya makantar da shi na wani dan lokaci.

Cikin wannan yanayi na karaji da kururuwa ta neman a kawo masa dauki, ya sanya nan da nan jami'an tsaro masu sintiri a hanyar suka cimma masu ta'adar biyu kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari. Ya ce an an cafke ababen zargin biyu tare da baburin mai kafa uku.

Masu kwacen biyu
Hakkin mallakar hoto: Jaridar The Nation
Masu kwacen biyu Hakkin mallakar hoto: Jaridar The Nation
Asali: UGC

KARANTA KUMA: Da yiwuwar allurar riga-kafin cutar korona za ta samu a karshen watan Yuni

Ya ce: "Da misalin karfe 7.55 na ranar 26 ga watan Mayun 2020, a yankin Umuogali da ke kan hanyar Onitsha zuwa Owerri, wasu 'yan ta'adda biyu da su ka yi kaurin suna wajen kwacen keke napep, sun shiga hannu."

An garkame 'yan ta'addan da suka shahara da satan keke a ofishin 'yan sanda na Oba da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra."

A Arewacin Najeriya kuma mun samu cewa, Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, ta kaddamar da bincike kan yawan mace macen da ake samu a jihar a baya bayan nan.

Masari ya ba da sanarwar hakan ne yayin gabatar da jawabai a taron manema labarai da gwamnatin jihar ta shirya don sanar da al’ummar jihar halin da ake ciki game da annobar cutar korona.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito gwamnan yana cewa, jihar Katsina na da kwararru da za su gudanar da bincike a kan lamarin don gano dalilin mace macen da ake samu a fadin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel