Kasafin kudi: Yan majalisa sun katse hutunsu na Sallah, sun koma majalisa cikin gaggawa

Kasafin kudi: Yan majalisa sun katse hutunsu na Sallah, sun koma majalisa cikin gaggawa

Yan majalisun dokokin Najeriya sun katse hutun Sallar da suke ciki don komawa bakin aiki cikin gaggawa domin yin nazari ga daftarin kwaskwararren kasafin kudin shekarar 2020.

Akawun majalisar, Muhammad Sani Omolori ne ya bayyana haka a ranar Talata, 26 ga watan Mayu, inda yace yan majalisar za su koma aiki ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Masari ya umarci ma’aikatan ilimi na jahar Katsina su koma aiki daga Laraba

“Ana sanar da Sanatoci da yan majalisar wakilai da cewa an sauya ranar komawa majalisa daga Talata, 2 ga watan, Yunin shekarar 2020 zuwa Alhamis, 28 ga watan Mayun shekarar 2020.

“An yi haka ne don baiwa yan majalisar daman yin nazari ga daftarin kudurin kwaskwararren kasafin kudin shekarar 2020, don haka ana bukatar Sanatoci da yan majalisu su hallara majalisa da karfe 10 na safiyar Alhamis, 28 ga watan Mayu.” Inji shi.

Dama yan majalisun sun tafi hutun makonni biyu ne don gudanar da bikin Sallah karama a garuruwansu.

Kasafin kudi: Yan majalisa sun katse hutunsu na Sallah, sun koma majalisa cikin gaggawa
Buhari, Lawan, Femi
Asali: Facebook

Amma shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bayyana akwai yiwuwar su koma aiki kafin karewar hutun da zarar sun samu sakon bangaren zartarwa game da kasafin kudin.

Premium Times ta ruwaito a watan Afrilun shekarar 2020 ne gwamnatin tarayya ta rage kasafin kudin bana daga naira tiriliyan 10.6 zuwa tiriliyan 10.3, inda ta rage N320bn.

Gwamnati ta yi haka ne sakamakon halin matsin tattalin arziki da aka samu sanadiyyar bullar annobar Coronavirus a duniya wanda ya karya farashin gangar danyen mai daga $57 zuwa $30.

Saboda haka ta rage kudin da take hasashen samu daga naira tiriliyan 8.4 zuwa naira tiriliyan 5.1, yayin da man da take fitarwa ya ragu daga ganga miliyan 2.2 zuwa ganga miliyan 1.7.

A wani labari kuma, Ma’aikatar ilimi ta gwamnatin jahar Katsina ta umarci ma’aikatanta su koma bakin aiki daga ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.

Katsina Post ta ruwaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in watsa labaru na ma’aikatara, Salisu Lawal Kerau ya fitar a ranar Talata, 26 ga watan Mayu.

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa ma’aikatan dake mataki na 10 zuwa sama ne kadai ake bukatar gani a wajen aiki, sauran su cigaba da zama a gida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng