Yawan mace mace a Katsina: Gwamna Masari ya kaddamar da bincike don gano dalili

Yawan mace mace a Katsina: Gwamna Masari ya kaddamar da bincike don gano dalili

Gwamnatin jahar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kaddamar da bincike kan yawan mace macen da ake samu a jahar Katsina a kulliyaumin.

Masari ya bayyana haka ne yayin da ya gabatar da jawabi a taron manema labaru da gwamnatin jahar ta shirya don sanar da al’ummar jahar halin da ake ciki game da cutar COVID-19.

KU KARANTA: Masari ya umarci ma’aikatan ilimi na jahar Katsina su koma aiki daga Laraba

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito gwamnan ya ce jahar Katsina na da kwararru da za su gudanar da bincike a kan lamarin don gano dalilin mace macen da ake samu a jahar.

“Kwararrun za su gudanar da bincike don gano abin dake sabbaba mace macen jama’a a jahar Katsina, yawancin wadanda suke mutuwa dattijai ne, kuma ba tare da zuwa asibiti ba.

“Kwararrun zasu dauki wasu samfurin abubuwan da ake bukata don yin gwaje gwaje daga gawarwakin mamatan domin a tabbatar idan mutuwar na da alaka da COVID-19 ko a’a.” inji shi.

Yawan mace mace a Katsina: Gwamna Masari ya kaddamar da bincike don gano dalili
Gwamna Masari Hoto: Katsinapost
Asali: Facebook

Haka zalika gwamnan ya ce gwamnatin jahar na da kimanin samfur 400 dake jiran a musu gwaji daga hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC.

Don haka gwamnan ya nemi jamian tsaro su cigaba da dabbaka dokar hana fita, zirga zirga, tafiye da tafiye da dokar zaman gida domin dakile yaduwar cutar a tsakanin al’ummar jahar.

A hannu guda kuma, Masari ya shawarci jama’an jahar su cigaba da bin matakan da gwamnati ta tsara, sa’annan ya bayyana kotunan tafi da gidanka za su cigaba da aiki.

Ma’aikatar ilimi ta gwamnatin jahar Katsina ta umarci ma’aikatanta su koma bakin aiki daga ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in watsa labaru na ma’aikatara, Salisu Lawal Kerau ya fitar a ranar Talata, 26 ga watan Mayu.

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa ma’aikatan dake mataki na 10 zuwa sama ne kadai ake bukatar gani a wajen aiki, sauran su cigaba da zama a gida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel