Masari ya umarci ma’aikatan ilimi na jahar Katsina su koma aiki daga Laraba

Masari ya umarci ma’aikatan ilimi na jahar Katsina su koma aiki daga Laraba

Ma’aikatar ilimi ta gwamnatin jahar Katsina ta umarci ma’aikatanta su koma bakin aiki daga ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.

Katsina Post ta ruwaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in watsa labaru na ma’aikatarta, Salisu Lawal Kerau ya fitar a ranar Talata, 26 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Tsuntsu daga sama gasashshe: PDP ta fara zawarcin babban gwamna a jam’iyyar APC

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa ma’aikatan dake mataki na 10 zuwa sama ne kadai ake bukatar gani a wajen aiki, sauran su cigaba da zama a gida.

Masari ya umarci ma’aikatan ilimi na jahar Katsina su koma aiki daga Laraba
Masari Hoto: Katsinapost
Asali: Facebook

“An umarce ni na sanar da ma’aikatan ilimi na jahar Katsina dake fadin jahar daga mataki na 10 zuwa sama da su koma bakin aiki daga ranar 27 ga watan Mayu na shekarar 2020.

“Sai dai komawar bai hada da makarantu ba, makarantu za su cigaba da zama a kulle har sai yadda hali ya yi. Don haka ana kira ga ma’aikatan su tabbata sun dabbaka dokokin yaki da yaduwar Coronavirus.

“Kamarsu wanke hannu, bayar da tazara, amfani da takunkumin kariya da kuma kauce ma shiga dandazon taron jama’a yayin taruka a wajen gudanar da aiki.” Inji shi.

A wani labari, Kansila dake wakiltar mazabar Galadama-Dangaladima a karamar hukumar Kaura-Namoda ta jahar Zamfara, Sagir Dansani ya ci dukan tsiya sa’annan aka masa tsirara.

Punch ta ruwaito kansilan ya bayyana haka ne daga gadon asibitin da yake jinya a garin Kaura Namoda, inda yace wasu miyagu ne suka dauke shi daga gidansa a ranar Asabar.

“Ba su tsaya ko ina ba sai sakatariyar karamar hukumar inda suka lakada min dan banzan duka, har sai da na fita hayyaci na,

"Koda na farfado, sai na tarar da ni tsirara haihuwar uwata, daga nan na shiga kuwwa ina neman taimako, shi ne aka garzaya da ni babban asibitin Kaura Namoda.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel