Babu gaskiya a batun cewa ana binciken ofishin Kyari – Inji Garba Shehu

Babu gaskiya a batun cewa ana binciken ofishin Kyari – Inji Garba Shehu

- Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan rade-radin da ke ta yawo a gari

- Ana jin kishin-kishin din cewa ana binciken aikin Marigayi Abba Kyari

- Hadimin Shugaban kasa, Garba Shehu, ya musanya wadannan rahotonni

A karshe fadar shugaban kasa ta maida martani ga rahotannin da ke kokarin nuna cewa Muhammadu Buhari ya mika ragamar mulkinsa ga marigayi Malam Abba Kyari.

A wani jawabi da babban hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya yi, ya bayyana cewa Muhammadu Buhari ne wanda jama’a su ka zaba, kuma shi ne mai wuka da nama.

Garba Shehu ya karyata rade-radin da ake ji na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni a soke duk wasu mukamai da Abba Kyari ya bada daf da zai kwanta jinya.

“Hankalin fadar shugaban kasa ya kai ga rahotanni a kafafen yada labarai cewa Muhammadu Buhari ya soke wasu takardu da tsohon shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa ya sa hannu a kai.

KU KARANTA: Ayyukan da Farfesa Gambari ya karya da su bayan gaje kujerar Kyari

Shehu ya na mai watsi da wadannan labarai a ranar Talata, 26 ga watan Mayu, 2020, ya ce: “Ba abin mamaki ba ne, ba a kama sunan kowa a matsayin majiyar wannan labari ba”

Mai magana da yawun bakin shugaba Buhari ya cigaba da cewa: “Babu daidai da kwayar gaskiya a cikin wadannan rahotanni, kuma ‘Yan Najeriya su yi da abin da ake nema.”

Domin sake tabbatar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ne mai cikakken ikon juya madafar gwamnati, Garba Shehu ya nuna akalar gwamnati ba ta kasance a hannun wani ba.

Shugaban kasa Buhari ne wanda ‘Yan Najeriya su ka sake zaba a kan mulki a watan Fubrairun 2019, bai taba ba, kuma ba zai taba mika mulki ga wani mutum dabam ba.” Inji sa.

Malam Shehu ya ce amana da kuma ikon da ‘Yan kasar su ka damkawa shugaban na su ba zai fada hannun kowa ba. Hadimin shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a tuwita.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel