Yanzu-yanzu: Jihar Kaduna ta sake tsawaita dokar hana zirga-zirga (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Jihar Kaduna ta sake tsawaita dokar hana zirga-zirga (Bidiyo)

Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ta bayyana karin makonni biyu a kan kulle da kuma dokar hana zirga-zirga a jihar.

Kamar yadda bidiyon da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na twitter ya bayyana, mataimakiyar gwamnan jihar, Dr Hadiza Balarabe ce ta bada sanarwar.

Kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana, da yawa daga cikin masu cutar a jihar duk daga wasu jihohi suka je suka kwaso.

"An gano cewa masu shige da fice cikin jihar ne ke kawo cutar. Matakin dakile cutar korona, kowa ne ya dace ya dauka don tseratar da rayuka," sanarwar tace.

Daukar mataki wanda zai zama kariya ga kowa daga muguwar annobar da ta game duniya.

Sanarwar ta kara da bayyana cewa, hatsarurrukan cutar korona basu wuce ba. Har yanzu cuta ce mai hatsari da tada hankali.

Wannan ne yasa dole 'yan kasa su jajirce tare da dakile yaduwar annobar ta hanyar kiyaye dokoki.

"Hatsarurrukan da ke tattare da cutar korona basu wuce ba. Har a halin yanzu cuta ce mai hatsari da tada hankali. Wannan ne yasa dole 'yan kasa su jajice wajen tabbatar da dakile muguwar cutar mai matukar hatsari," takardar tace.

KU KARANTA: Katsina: Sama da mutum 600 suka samu mafaka a filin kwallo bayan harin 'yan bindiga (Hotuna)

Rundunar sojin hadin guiwa (MNJTF) ta ragargaji mayakan ta'addancin ISWAP a yankunan tsibirin tafkin Chadi, kamar yadda majiya daga rundunar ta sanar.

"Bayan samun bayanan sirri daga majiyoyi daban-daban, mun samu bayanai inda 'yan ta'addan suka rike a Tumbun tare da gano sansani, wurin adana makamai da sauran abubuwan amfanin 'yan ta'addan.

"Dogaro da hakan, dakarun sun kai samame ta jiragen yaki, an ragargaza ababen amfanin 'yan ta'addan," majiyar tace.

Sakamakon samamen ya bayyana cewa an halaka 'yan ta'addan masu tarin yawa tare da kona gine-ginen 'yan ta'addan.

Tashin bama-bamai daga bidiyon ya bayyana cewa an kone ababen hawa da ma'adanar man fetur din 'yan ta'addan.

Hakazalika, jiragen yakin kasar Chadi sun kai samame a Tumbun, shugaban fannin yada labarai na dakarun kasar Chadi, Kanal Timothy Antigha, yace a wata takarda.

Antigha ya kara da cewa: "A kwanaki masu zuwa, dakarun kasar tare da na MNJTF za su tsananta kokarinsu wajen murkushe ragowar 'yan ta'adda.

"Wannan kokari ne don dakile duk wani hari da mayakan ISWAP za su iya kawowa yankin da MNJTF din suke."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng