Datse iyakar Kaduna da Kano: El-Rufai ya kai samame kuwa ranar Sallah?

Datse iyakar Kaduna da Kano: El-Rufai ya kai samame kuwa ranar Sallah?

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya kwashe ranakun Juma'a da Asabar a kan iyakar jihar Kano da Kaduna don tabbatar da dokar hana zirga-zirga a tsakanin jihohin.

Tuni dai El-Rufai ya lashi takobin cewa babu wanda zai shiga jihar Kaduna daga Kano bayan matakin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dauka na ci gaba da yin sallar Juma'a da kuma Idi a jiharsa.

Zuwa yanzu dai, a hukumance gwamnatin jihar Kaduna ba ta bayyana adadin ababen hawan da gwamnan ya tare ba ko ya mayar da su inda suka fito a tsayuwar da ya yi a kan iyakar.

Sai dai kuma, wasu hotuna da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter, sun nuna gwamnan na tattaunawa da direbobin motocin sannan kuma akwai cunkoson ababen hawa a iyakar jihohin.

Hakazalika, gwamnatin jihar Jigawa ta koka a kan yadda almajirai suke kai mata karin cutar korona daga jihar Kano.

KU KARANTA: Boko Haram: MNJTF sun ragargaza mayakan ta'addanci ta jiragen yaki

Kafin nan, Gwamna El-Rufai ya maimaita cewa mafi yawan masu cutar a jiharsa almajirai ne da Ganduje ya dawo dasu jihar Kaduna. Lamarin da ya kawo cacar baki tsakanin gwamnonin biyu.

A martanin Ganduje da ya bada ta sanarwar, ya ce "Yadda muke mayar da almajirai jihohinsu, haka mu ma ake dawo mana da almajirai 'yan asalin jihar Kano daga wasu jihohin."

"Don ba ma yin surutu a kan batun, ba yana nufin dukkansu lafiyayyu bane ake dawo mana dasu."

Duk da ana zargin wata jikakkiya tsakanin Gwamnonin biyu, babu wanda zai ce ga takamaiman abinda ya hada su, sai dai hasashe.

Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta jihar Kano ta tabbatar da cewa mutum 896 ke dauke da cutar korona. Mutum 36 suka rasa rayukansu. Ita ce jiha kan gaba a yawan masu korona a fadin arewacin Najeriya. Ita ke takewa jihar Legas baya a fadin Najeriya.

A daya bangaren, jihar Kaduna na da mutum 189 da aka tabbatar suna dauke da muguwar cutar kamar yadda NCDC ta tabbatar. An rasa mutum biyar amma mutum 116 aka sallama daga asibiti.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel