Sauke Shugaban TCN daga kujerarsa ya raba kan Boss Mustafa da Ibrahim Gambari

Sauke Shugaban TCN daga kujerarsa ya raba kan Boss Mustafa da Ibrahim Gambari

- Kwanakin baya ne shugaban kasa Buhari ya tsige Shugaban kamfanin TCN

- Wannan abu bai yi wa Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa dadi ba

- Ana zargin har hakan ya jawo sabani tsakanin Ibrahim Gambari da Mustafa

Sauke shugaban kamfanin raba wutar lantarki da aka yi daga kan kujerarsa, ya haddasa fada tsakanin sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Jaridar Daily Sun ta fitar da rahoto cewa ana samun matsala tsakanin Boss Mustapha da farfesa Ibrahim Gambari da kungiyar kwadago a dalilin tsige shugaban kamfanin lantarkin.

Kungiyar kwadago ta na zargin Boss Mustapha ya nuna rashin goyon bayansa game da matakin da shugaban kasa ya dauka ta ofishin Ibrahim Gambari wajen sauke shugaban TCN.

A makon jiya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cire Usman Gur Mohammed daga kujerarsa da sunan yi wa sha’anin wutar lantarki garambawul a kasar, ya nada Sure Abdulaziz.

Jim kadan bayan tsige Usman Gur Mohammed, ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya fitar da takarda, ya na jan hankalin ministoci ya kamata a sanar da shi kafin a dauki matakin.

KU KARANTA: Ayyukan da Farfesa Gambari ya fara da su bayan hawa kujerar COS

Sauke Shugaban TCN daga kujerarsa ya raba kan Boss Mustafa da Ibrahim Gambari
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustafa Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Boss Mustapha a takardar da ya aikawa ministocin kasar, ya soki sauke shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya da ake yi haka kawai, ya ce wannan ya na da illa.

A cikin wannan takarda, Boss ya fadawa ministocin kai-tsaye cewa ba su da karfin ikon sallamar duk wani CEO ba tare da shugaban kasa ya ladabtar da shi idan har ya aikata laifi ba.

Wasu masu ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki sun fito sun nuna cewa SGF din ya na kokarin fada ne da ministan lantarki, Saleh Mamman wanda kamfanin TCN ke karkashinsa.

Majiyar ta kare ministan, ta ce shi ne wanda aka wakilta ya yi aikin inganta wutar lantarkin kasar. ‘Yan kwadagon su na ganin martanin Boss kamar takalar fadar shugaban kasa.

Ganin cewa shugaba Buhari ya bukaci duk wata takarda ta fito daga COS, kungiyar ta na ganin Boss ya shiga hurumin da ba na sa ba, kuma ta yi gargadi kan dawo da Gur Mohammed.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel