Sallar Idi: 'Yan sanda sun kama manyan malamai 3 a Zaria

Sallar Idi: 'Yan sanda sun kama manyan malamai 3 a Zaria

Jami'an 'yan sanda a karamar hukumar Zaria sun damke malaman addinin Musulunci 3 a tsakanin Juma'a zuwa Lahadi sakamakon zarginsu da ake da jan sallar Idi da na Juma'a.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, an gayyaci malamai biyu don tuhuma tare da amsa tambayoyi a kan sallar Idin da suka ja a ranakun Asabar da Lahadi da suka gabata.

Sani Halifa shugaba ne a malamai mabiya darikar Tijjaniya a garin Zaria. Ya ja sallar idi a ranar Asabar bayan umarnin shugaban darikar Tijjaniya na kasa, Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya tabbatar da cewa ranar Asabar ce daya ga watan Shawwal.

An gano cewa jami'an 'yan sanda sun kira tare da tuhumar malamin don ya wanke kansa.

An kama wani malami mai suna Sardauna Limamin Bizara a ranar Lahadi bayan ya ja sallar Idi a kauyen Bizara da ke Zaria. An sake sa bayan tuhumarsa da aka yi.

An kama Malam Muhammad Tukur Idris a ranar Juma'a bayan ya ja sallar Juma'a a wani karamin Masallaci da ke kan titin Agoro zuwa gaskiya.

Bincike ya bayyana cewa malamin na hannun sashin bincike na musamman na rundunar 'yan sanda da ke jihar Kaduna bayan kama shi da aka yi.

Sallar Idi: 'Yan sanda sun damke manyan malamai 3 a Zaria
Sallar Idi: 'Yan sanda sun damke manyan malamai 3 a Zaria. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An sako malamin addinin musulunci da aka kama saboda 'zagin' El-Rufa'i

A wata tattaunawa da aka yi tare da duba masallacin, an gano cewa ba zai kwashi ko mutum 20 ba a lokaci daya.

Daya daga cikin wadanda suka bi jam'in ya bayyana cewa, "A gaskiya masallacin na salla ne ba sallar Juma'a ba.

"Amma kuma saboda rashin yin sallar Juma'a na makonni tara, mun bukaci malamin da ya ja mu sallar. A kalla zamu ce mun yi sau daya a watan Ramadan.

"A gaskiya ba limamin masallacin Juma'a bane. An mika bukatar ne a gabansa kuma ya amsa mana. Kamar yadda kuka sani, a dukkan arewacin Najeriya, jihar Kaduna ce kadai ta kwashe makonni tara ba a yi salla ba da sunan korona.

"Muna rokon gwamnan da ya saki limamin. Muna son zaman lafiya shiyasa muke biyayya ga gwamnati. Amma tozarta limamanmu ba zai tabbatar mana da zaman lafiya ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel