Yadda ta ke kayawa da Farfesa Ibrahim Gambari a fadar Shugaban kasa

Yadda ta ke kayawa da Farfesa Ibrahim Gambari a fadar Shugaban kasa

Sabon hadimin shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya na cigaba da gyara zama a ofishinsa a Najeriya. Jaridar Daily Trust ta duba yadda abubuwa su ke kankama a halin yanzu.

Ibrahim Gambari ya shiga ofis ne a ranar 13 ga watan Mayu, 2020. Aikin farko da ya yi shi ne halartar taron FEC na majalisar zartarwar tare da shugaban kasa da ministocin tarayya.

Bayan taron FEC na mako-mako, Gambari ya gana da mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Janar Babagana Monguno tare da jami'in fadar shugaban kasa, Tijjani Umar.

Jaridar ta ce ziyarar da Ibrahim Gambari ya kai ofishin Babagana Monguno ya nuna cewa manyan hadiman shugaban kasar za su yi aiki tare, akasin abin da ya rika faruwa a baya.

Ranar Alhamis ne Farfesa Gambari ya halarci taron majalisar tsaro na NSC. Washegari kuma ya na cikin wadanda su ka tarbi tawagar shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo.

KU KARANTA: Malamai sun yi wa sabon Hadimin Shugaban kasa, Gambari addu'o'i

Yadda ta ke kayawa da Farfesa Ibrahim Gambari a fadar Shugaban kasa
Farfesa Ibrahim Gambari. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

A ranar 19 ga watan Mayu, rahotanni su ka tabbatar da cewa Ibrahim Gambari ya gana da Rt. Hon. Femi Gbajabiamila inda shugaban majalisar wakilan ya kawo masa ziyarar farko a ofis.

Kafin nan kuma sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar ya shirya wani zama da aka yi tsakanin Janar TY Danjuma da shugaban kasa, wanda shi ne na farko tun shekarar 2017.

Bayan haka Gambari ya san da labarin sallamar shugaban kamfanin TCN na kasa, Usman Gur Mohammed. Gwamnatin taratta ta tsige Mohammed ne kwanaki biyar da shigar COS ofis.

Bugu da kari, ana rade-radin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci a soke duk wasu nade-naden mukamai da marigayi Abba Kyari ya yi daf da zai kwanta rashin lafiya.

Rahoton ya bayyana cewa zai yi wahala a iya tantance inda Ibrahim Gambari ya sa gaba a daidai lokacin da cutar COVID-19 ta tsaida abubuwa, sai dai an ce mutum ne shi mai faram-faram.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel