COVID-19: Marasa lafiya sun yi gardamar a kula da su a Gombe - Kwamiti

COVID-19: Marasa lafiya sun yi gardamar a kula da su a Gombe - Kwamiti

Jaridar The Punch ta rahoto cewa akalla marasa lafiya 30 ake tunanin sun kauracewa dakunan killace masu jinyar cutar COVID-19 a jihar Gombe.

A ranar Litinin, shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 a Gombe, farfesa Idris Mohammed, ya shaida cewa mutum 12 ne kadai ake da labarinsu.

Ragowar mutane kimanin 18 ba su cikin dakunan killace masu fama da COVID-19 a jihar Gombe kamar yadda Idris Mohammed ya fadawa ‘yan jarida.

Farfesa Idris Mohammed ya ce: “Mu na da jimillar mutane 30 da ba a dauke ba a Gombe, daga cikinsu biyar ainihin mutanen jihar Adamawa ne.”

“Mun dauki jininsu mun yi masu gwaji, amma sun koma Adamawa. Saboda an dauki alkaluma, ana sa su cikin marasa lafiyanmu, amma su na Adamawa.”

KU KARANTA: Katsina ta yi wa jihar Legas rakiya a alkaluman masu COVID-19

COVID-19: Marasa lafiya sun yi gardamar a kula da su a Gombe - Kwamiti
Gwamnan Jihar Gombe. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

“An gano wasu mutane biyu sun fito ne daga Kano, mun fadawa likitan jihar kuma an killace su; daya kuma ya na Ogun, mun gano guda ya na Nasarawa.”

Shugaban kwamitin ya ce: “Na karshen mutumin Borno ne, mun maida shi jiharsa.” Kwamitin ta ce ta na kokarin ganin ba a yadawa jama’a wannan cuta ba.

“Mutane 20 da su ka rage su ke kawo mana cikas, amma mu na kokarin maida su. A Lahadi, mun dauke biyu. Abin murnar shi ne sun killace kansu da kansu.”

Mohammed ya ce jihar Gombe ta na aiki da jihohin da wadannan mutane su ka fito wajen ganin an killacesu a inda su ke domin ayi masu maganin COVID-19.

“Sarakuna da shugabannin inda su ke su na aiki da kwamitin yaki da COVID-19 domin tabbatar da cewa an tsaresu, an yi masu magani kafin a sake su.” inji sa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel