Buhari ya aikawa Iyali, NUJ, NGE, ta’aziyyar mutuwar Waheed Bakare

Buhari ya aikawa Iyali, NUJ, NGE, ta’aziyyar mutuwar Waheed Bakare

- Daya daga cikin manyan ‘yan jaridar Najeriya, Waheed Bakare ya rasu

- Mr. Waheed Bakare ya cike ne a Ranar Lahadi, 24 ga watan Mayun 2020

- Shugaban kasa ya yi ta’aziyyar rasuwar Editan Jaridar New Telegraph

Jaridar New Telegraph ta yi rashin babban Editanta ta ranar Asabar, mista Waheed Bakare wanda ya cika bayan ya yi fama da ‘yar gajerar rashin lafiya.

Waheed Bakare ya yi numfashin karshe ne a yammacin ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu, 2020. Kawo yanzu ba mu da labarin cutar da ta kashe ‘dan jaridar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce mutuwar Bakare babban rashi ne ga gidan jarida. Shugaban kasar ya yi jawabi ne ta bakin mista Femi Adesina.

Femi Adesina wanda ke taimakawa shugaban kasar wajen yada labarai da hulda da jama’a ya yi wa kungiyar ‘yan jaridar Najeriya ta NUJ ta’aziyyar rashin.

KU KARANTA: Mutane 8, 000 su ke dauke da cutar Coronavirus a Najeriya

Haka zalika Adesina ya aikawa kungiyar NGE ta Editocin kasar sakon ta’aziyyar mutuwar Bakare. Marigayin ya kasance cikin ‘ya ‘yan wadannan kungiyoyin.

Muhammadu Buhari ya yi addu’a Ubangiji ya jikan Waheed Bakare, sannan ya rokawa ‘yanuwa da abokan arzikin marigayin samun jure rashin da su ka yi.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana daga jaridar The Sun, marigayi Bakare ya zama Editan jaridar New Telegraph ne shekaru kusan biyar da su ka wuce.

Waheed Bakare ya saba bayyana a gidajen talabajin domin cire jama’a daga rudu. Masu kallon hirar ‘yan jarida a tashar TVC, sun saba ‘ganin Waheed Bakare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel