Mu na kashe N4,500 domin ciyar da kowanne mai cutar korona a kowacce rana - Bala Kaura

Mu na kashe N4,500 domin ciyar da kowanne mai cutar korona a kowacce rana - Bala Kaura

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta na kashe N4,500 domin ciyar da kowanne mai cutar korona da aka kai cibiyar killace ma su cutar a jihar.

Rilwanu Mohammed, shugaban kula da cigaban harkokin lafiya a matakin farko, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Lahadi.

Ya ce gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ne ya bayar da umarnin a tabbatar cewa ana bawa masu cutar korona a cibiyar isashen abinci.

Wasu daga cikin ma su korona sun yi zanga - zanga domin nuna rashin jin dadinsu a kan yadda aka barsu kara zube a cibiyar killacewa.

Mohammed, shugaban bin diddigin ma su cutar korona a jihar, ya ce gwamna ya bayar da umarnin a tabbatar da cewa ma su cutar sun ji tamkar a gida su ke yayin da su ke cibiyar.

Mu na kashe N4,500 domin ciyar da kowanne mai cutar korona a kowacce rana - Bala Kaura
Gwamnan jihar Bauchi: Bala Mohammed
Asali: Facebook

"Gwamna ne ya bayar da umarnin cewa ake kashe N1,500 a kowanne kwanon abinci da za a bawa mai cutar korona a cibiyar killacewa a kowacce rana.

DUBA WANNAN: Babu wata nesanta: Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a Kano

"Hakan na nufin za a kashe N1,500 a abincin kumallo, da na rana da kuma abincincin dare saboda ba ya son wani mutum a cibiyar killacewa ya yi korafin cewa ba ya samun kulawa kamar yadda ta ke faruwa a wasu jihohi.

"Idan aka lissafa za a ga cewar ana kashe jimillar N4,500 domin ciyar da kowanne mai cutar korona da ke cibiyar killacewa a kowacce rana," a cewar Mohammed.

Mohammed ya bayyana cewa ya sha samun kira daga wurin mutane ma su lafiya domin rokon a kaisu cibiyar killacewa domin su ke morar irin abincin da ake bayarwa a cibiyar killacewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel