Sojoji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram 1000 - Buratai

Sojoji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram 1000 - Buratai

Babban hafsan rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Yusuf Buratai, ya ce dakarun rundunar soji sun kasahe mayakan kungiyar Boko Haram da takwarorinsu na ISWAP 1,015 a cikin sati shidda da su ka gabata.

Buratai ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya ke gabatar da jawabi a wurin taron da rundunar atisayen Ofireshon LAFIYA DOLE ta shirya a Maiduguri.

Ya bayyana cewa, a tsawon lokacin, an kama jimillar manyan mambobin kungiyar Boko Haram 84 tare da 'yan leken asirin kungiyar da kuma kayansu na amfani.

"Mun kara kaimi wajen yaki da mayakan kungiyar Boko Haram da na ISWAP. Mun tumurmusa mambobin kungiyoyin, mun samu nasarar lalata sansaninsu ma su yawa.

"Mun kashe mayakan kungiyoyin 1015 a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa. Mun kama 'yan kwangila da 'yan leken asirin kungiyoyin 84 a atisayen da mu ka fara tun ranar 12 ga watan Afrilu," a cewar Buratai.

Dakarun soji na cigaba da kaddamar da manyan hare - hare tare da samun galaba a kan 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram da ISWAP a karkashin atisayen KANTANA JIMLAN wanda shugaban rundunar soji, laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya kaddamar domin tsananta yaki da 'yan ta'addar.

Sojoji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram 1000 - Buratai
Buratai
Asali: UGC

A irin wadannan zafafan hare - haren da dakarun soji ke kaiwa, sun kai wani hari a wata maboyar 'yan ta'adda da ke kan hanyar zuwa Adzunge.

Ba a kama kowa ba yayin harin saboda 'yan ta'addar sun tsere bayan sun hango rundunar sojoji ta tunkaro kauyen.

Sojojin sun samu kayan amfanin 'yan ta'addar da su ka hada da babur guda biyu da wani babban injin nika nikan lausi, wanda aka fi sani da 'Lister'.

DUBA WANNAN: Dalilinmu na yin Sallar Idi ranar Juma'a bayan yin azumi 29 - 'Yan Shi'ar Najeriya

A ranar 13 ga watan Mayu a yankin Pulka, rundunar soji ta kai harin kwanton bauna a kan wasu mayakan kungiyar Boko Haram a yayin da su ke gudun hijira daga dajin Sambisa zuwa tsaunin Mandara.

Dakarun soji sun kashe biyar daga cikin 'yan ta'addar sannan sun samu bindigu kirar AK47 guda uku, wata jaka mai dauke da kakin 'yan kungiyar Boko Haram da sauran wasu alburusai bayan na cikin bindigun da aka kama.

Sojoji sun mayar da martani da karfinsu yayin wani harin kwanton bauna da 'yan Boko Haram su ka kai mu su a kauyen Gajigana a ranar 18 ga watan Mayu.

Kokarin mayakan na guduwa, bayan sun kwashi kashinsu a hannu, bai yi nasara ba, saboda sojojin da aka turo kawo agaji sun yi zafin nama wajen datsesu a hanya da kuma kama makaman da ke tare da su.

Makaman sun hada da bindigun AK47 guda biyu, alburusai, gurneti da bam samfurin LG3.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel