Buhari ya haramta wa ministoci hukunta shugabannin cibiyoyi da ke karkashinsu

Buhari ya haramta wa ministoci hukunta shugabannin cibiyoyi da ke karkashinsu

Gwamnatin shugaba Buhari ta haramta wa ministocinta sallamar shugabannin cibiyoyin da ke karkashin su kai tsaye.

A halin yanzu, sabon tsarin ya kara karfafa ikon ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta fuskar ladabtarwa, kamar yadda wata takarda da Premium Times ta gani.

Takardar mai kwanan wata 19 Mayu wacce kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya aminta da ita, ya nuna tsananin damuwarsa a kan yadda ministoci ke tsige shugabannin wasu cibiyoyi da ke karkashin su da kuma illar hakan ga daidaituwar cibiyoyin.

An tura takardar ga kowanne ministan da kuma sauran manyan jami'an gwamnatin wadanda suka hada da shugabar ma'aikatar tarayya, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, shugabannin tsaro, gwamnan babban bankin Najeriya da kuma manyan sakatarorin gwamnati.

A baya, ministoci na da karfin ikon ladabtar da shugabannin kungiyoyi, hukumomi ko sashen da suke kula dasu. Ladabtarwar na kamawa daga dakatarwa da kuma kora kwata-kwata.

Buhari ya haramta wa ministoci sallama ko hukunta shugabannin cibiyoyin da ke karkashinsu
Buhari ya haramta wa ministoci sallama ko hukunta shugabannin cibiyoyin da ke karkashinsu. Hoto daga Premium Times
Asali: Twitter

A misali, a watan Janairu, ministan wutar lantarki, Sale Mamman ya tsige Damilola Ogunbiyi da Marilyn Amobi a matsayin shugabannin cibiyar wutar karkara ba tare da sanin fadar shugaban kasa ba ko kuma gurfanarsu a gaban kwamitin ladabtarwa.

DUBA WANNAN: Ba a ga wata ba a Najeriya, Idi sai ranar Lahadi –Sarkin Musulmi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya so dawo da su kan aikinsu amma kuma sai ministan ya sake korar manajan daraktan kamfanin rarrabe wutar lantarki na Najeriya, Usman Mohammed, tare da wasu daraktoci hudu, duk da yace ya nemi izinin shugaba Buhari.

Wannan takardar da sakataren gwamnatin tarayyar ya fitar na bada kariya ga shugabannin cibiyoyi daga ministocin da ke kula da su, don hakan ne kadai zai dakatar ko hana sallamarsu a yayin da wani abu ya taso.

Hakazalika, barazanar ministoci na kora matukar aka kama shugaban cibiya da rashin daukar aikinsa da muhimmanci ba zai yi aiki ba yanzu.

Kamar yadda takardar ta bayyana, idan shugaban cibiya ya yi laifi, ana bukatar ya mika koken ta hannun babban sakatarensa zuwa majalisar zartarwar cibiyar don fuskantar hukuncin da ya dace.

Daga nan ne majalisar zartarwar za ta iya mika wasikar tuhuma ko kuma ta shawarci ministan a kan abinda ya dace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel