Kano: Yadda aka cika makil a masallatan Juma'a (Hotuna)

Kano: Yadda aka cika makil a masallatan Juma'a (Hotuna)

Dubban jama'a ne suka samu halartar sallar Juma'a a birnin kano da kewaye bayan makonni kusan biyar da aka yi da rufe wuraren bauta a jihar sakamakon barkewar annobar korona.

Kano: Yadda aka cika makil a masallacin Juma'a (Hotuna)
Kano: Yadda aka cika makil a masallacin Juma'a (Hotuna). Hoto daga BBC Hausa
Asali: Twitter

A yayin da BBC ta zanta da wasu daga cikin wadanda suka samu damar halartar sallar Juma'ar, sun bayyana tsananin farin cikinsu da yadda Allah ya basu damar komawa bauta.

Kano: Yadda aka cika makil a masallacin Juma'a (Hotuna)
Kano: Yadda aka cika makil a masallacin Juma'a (Hotuna). Hoto daga BBC Hausa
Asali: Twitter

Za a iya alakanta cikar masallatan Juma'ar a yau saboda wannan ce Juma'a ta karshe a wannan watan na Ramadan mai dumbin alfarma.

KU KARANTA: Allah ya yi wa babban dan kasuwar jihar Katsina, Alhaji Danmarke, rasuwa

Kano: Yadda aka cika makil a masallacin Juma'a (Hotuna)
Kano: Yadda aka cika makil a masallacin Juma'a (Hotuna). Hoto daga BBC Hausa
Asali: Twitter

Hakazalika, a masallatan an ga 'yan agaji na kokarin bai wa jama'a sinadarin tsaftace hannaye don biye wa dokar masana kiwon lafiya.

Kano: Yadda aka cika makil a masallacin Juma'a (Hotuna)
Kano: Yadda aka cika makil a masallacin Juma'a (Hotuna). Hoto daga BBC Hausa
Asali: Twitter

Wasu daga cikin masallatan na sanye da takunkumin fuska, sune kuwa aka bari shiga cikin masallacin.

Wadanda basu sanye da takunkumin fuska kuwa an bar su a farfajiyar masallatan.

Kano: Yadda aka cika makil a masallacin Juma'a (Hotuna)
Kano: Yadda aka cika makil a masallacin Juma'a (Hotuna). Hoto daga BBC Hausa
Asali: Twitter

A wani labari na daban, A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a sake tura tawagar kwararru jihar Kogi don tabbatar da cewa an samar da abubuwan da jihar ke bukata wajen yaki da cutar coronavirus.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bada wannan sanarwan a Abuja ga taron manema labarai yayin da suke tattaunawa da kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar shugaban kasa.

Idan za mu tuna, gwamnatin jihar ta hana NCDC bincike ko tallafa mata wajen shirya wa cutar coronavirus a yayin da suka ziyarci jihar.

Wannan zargin ya kawo rashin jituwa tsakanin jami'an NCDC din da jihar Kogi inda jami'an suka bar jihar ba tare da bin dokar gwamna Yahaya Bello ba.

Bayan wannan ci gaban, Ehanire ya ce kwamitin zai tattauna da gwamnan tare da yin aiki da shi don samun hadin kan da zai bai wa NCDC damar yin aikinsu.

Ministan yace ma'aikatar za ta yi aiki tare da jihar don samar da hanyar inganta sadarwa da kuma mika koke.

Ehanire ya ce tawagar bincike da ta sauka jihar Cross River ta dawo kuma ta gano yankunan da ke bukatar kulawa a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel