Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya (Hotuna)

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya (Hotuna)

Duniya cike ya ke da attajirai da suke sanaoi mabanbanta kuma suka tara arziki mai yawa da hakan yasa sauran mutane ke neman zama kamansu.

Sai dai a wannan rubutun ba kansu zai mayar da hankali ba, zai mayar da hankali ne a kan wasu attajirai 10 da suka fi kowa arziki a tarihin duniya kamar yadda Legit.ng ta samo daga money.com

10. Ghenghis Khan

Ghengis Khan na daular Mongolia ya yi rayuwa ne tsakanin 1162 da 1227. Kwamandan soja ne kuma an ce mutum ne mai yawan kyauta.

A cewar masu nazarin tarihi, Khan bai taba boye dukiyarsa ba.

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya
Ghengis Khan. Hoto daga Getty Images
Asali: Getty Images

9. Jeff Bezos

A lokacin da aka tattara wannan jerin sunayen a 2014, attajirin dan kasuwa Bill Gates shine mutum na 9 cikin jerin masu kudi amma Bezos ya maye gurbinsa tunda ya dara shi kudi a yanzu.

Bezos ne mai kamfanin Amazon. An haife shi ne a ranar 12 ga Janairun 1964. Dukiyarsa ta kai Dallan Amurka biliyan 147.4

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya
Jeff Bezos. Hoto daga Bigography.com
Asali: Twitter

8. Alan Rufus wanda aka fi sani da Alan The Red

Alan Rufus dan uwan William the Conqueror ne. An ce tare da kawunsa a suka ci garin Norman da yaki.

A cewar Philip Beresford da Bill Rubinstein, Rufus ya mutu ya bar fam 11,000. Hakan ya yi daidai da Dalla biliyan 194 a shekarar 201

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya
Alan Rufus. Hoto daga Bodleian Library Oxford—The Art Archive
Asali: UGC

7. John D. Rockefeller

John D. Rockefeller ya yi rayuwa tsakanin 1839 da 1937.

Ya fara saka hannun jari a fanin man fetur a 1863 kuma a shekarar 1880 kamfaninsa mai suna Standard Oil ce ke kula da kashi 90 cikin 100 na man fetur din Amurka.

A cewar New York Times, an kiyasta arzikin Rockefeller a ya kai Dalla biliyan 1.5. Kwatankwacin Dalla Biliyan 341 a shekarar 2014.

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya
John D. Rockefeller. Hoto daga Seattle Times/JR Partners—Getty Images
Asali: Getty Images

6. Andrew Carnegie

Andrew Carnegie ya yi rayuwa tsakanin 1835 da 1919 kuma kiyashin arzikinsa ya kai Dalla biliyan 372.

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya
Andrew Carnegie.
Asali: UGC

5. Joseph Stalin

Joseph Stalin ya yi rayuwa tsakanin 1878 da 1953.

A lokacin yana raye, shi ya ke kula da dukiyar USSR wacce a lokacin suke da kashe 9.6 na arzikin duniya. Kwararrun masana tattalin arziki da dama sun lissafa shi cikin masu arzikin duniya don abu ne mai wuya banbanta kudinsa da na kungiyar tarayyar kasashen USSR.

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya
Joseph Stalin. Ullstein Bild—Getty Images
Asali: Getty Images

4. Akbar I

Akbar I ya yi rayuwa tsakanin 1542 da 1606. Ya mulki daular Mughal ta kasar India wacce a lokacin ta ke da kashi 25 cikin 100 na arzikin duniya.

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya
Akbar I. Hoto daga Peter Newark Pictures—Bridgeman Images
Asali: UGC

3. Sarki Shenzong

Sarki Shenzong ya yi rayuwa tsakanin 1048 zuwa 1085. Ya mulki daular Song ta kasar China wacce ke da arzikin duniya da ya kai kashi 25 zuwa 30 cikin 100.

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya
Emperor Shenzong. Hoto daga Bridgeman Images
Asali: UGC

2. Augustus Caesar

Augustus Caesar ya yi rayuwa tsakanin 63 BC da 14 AD a kasar Rome. Arzikinsa ya kai Dalla tiriliyan 4.6.

Shi ke kula da daular da ke da kashi 25 zuwa 30 cikin 100 na duniya a wancan lokacin.

Arzikinsa ya kai kwatankwacin Dalla tiriliyan 4.6 na shekarar 2014.

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya
Augustus Caesar. Hoto daga Hoberman Collection—UIG via Getty Images
Asali: Getty Images

1. Mansa Musa

Mansa Musa wanda ya yi rayuwa tsakanin 1280 zuwa 1337 shine mutum da ya fi kowa arziki a duniya. Arzikin da Sarkin daular Mali ya wuce yadda kowanne mahaluki ke kwatantawa.

Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya
Mansa Musa. Hoto daga Pinterest
Asali: UGC

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel