Matawalle ya ware N60m saboda gasar addinin musulunci ta bana a Zamfara

Matawalle ya ware N60m saboda gasar addinin musulunci ta bana a Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ba da sanarwar ware Naira miliyan 60 domin yin tanadin kyaututtukan da za a lashe a gasar ilimin addinin Islama na bana.

Matawalle ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun hadiminsa na musamman mai kula da hulda da al'umma, Zailani Bappa.

Cikin sanarwar da Malam Bappa ya gabatar a birnin Gusau ya ce, tsara gasar karatattukan na addinin Islama ya rataya ne a wuyan gidajen rediyo da ke fadin jihar.

Gwamna Matawalle ya ba da wannan sanarwar ne yayin gabatar da kyaututtuka ga wadanda suka lashe gasar da aka saba gudanarwa a watan Ramadan ta shekara-shekara a harabar gidan Rediyon jihar Zamfara.

Matawallen Maradun ya nuna farin ciki matuka a kan kwazon wadanda suka yi nasara a gasar bana, wadda aka gudanar ta hanyar wayar tarho kuma aka yada ta kai tsaye a gidajen Rediyo.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Gwamnan ya ba da umarnin a yanzu a rika gudanar da gasar ta shekara-shekara a kowane wata.

Gwamnan jihar Zamfara; Muhammad Bello Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara; Muhammad Bello Matawalle
Source: UGC

Gwamnan ya yi alkawarin sakin Naira miliyan 5 a kowane wata domin shirin, inda masu gasar za su fafata ta hanyar wayar tarho kuma a yada a gidajen Rediyo karkashin kulawarsa.

KARANTA KUMA: Pantami ya yabi gwamnonin da suka karbi kudirin rage kudin sadarwa na RoW

Yayin sake jaddada umarnin gudanar da gasar a kowane wata ba tare da an samu wani akasi ba, gwamnan yace ko da ta kasance wani uzuri ya sa ba ya jihar, to kuwa mataimakinsa ko kuma sakataren gwamnatinsa za a samu wanda zai kula da ita.

Gwamnan, wanda ya jagoranci shirin gasar da aka gudanar a makon da ya gabata, ya ba da kyaututtuka daban-daban, wadanda suka hada da motoci, babura masu kafa uku, kekunan dinki da tsabar kudi tsakanin N150,000 zuwa N300,000.

Ana iya tuna cewa, kimanin shekaru takwas da suka gabata, Kungiyar 'Yan Jaridu ta Nijeriya (NUJ) reshen jihar, Kungiyar Ma'aikatan Gidajen Rediyo da na Talbijin (RATTAWU) da Cibiyar Hulɗa da Jama'a ta Najeriya (NIPR) su ne suka fara tsara wannan shiri.

Ana gudanar da irin wannan gasa ta hanyar kiran waya, inda duk wanda ya kira zai zabi lamba, sai kuma a karanto masa tambaya mai dauke da wannan lamba, kuma idan mutum ya amsa daidai sai a fada masa kyautar da aka yiwa wannan tambaya tanadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel