Duk wanda ya shiga yajin aiki a bakacin aikinsa – El-Rufai ga jami’an kiwon lafiya
Yayin da ma’aikatan kiwon lafiya ke shirin shiga yajin aiki a Kaduna, gwamnati ta bayyana cewa za ta cigaba da bude cibiyoyin kiwon lafiyar tare da kare ma’aikatan dake son zuwa aiki.
Gwamnatin ta bayyana haka ne a matsayin martani ga kokarin shiga yajin aiki da ma’aikatan ke yi, inda ta ce ba za ta lamunci duk wani bita da kulli daga wajen ma’aikatan ba.
KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi gwamnoni game da tsangwamar almajirai
Don haka tace bata amince da yajin aikin ba, kuma duk wanda bai je aiki ba ya yi asarar aikinsa kenan domin kuwa za’a dauki sunan kowanne ma’aikaci a ma’aikatar kiwon lafiya.
A dalilin haka gwamnati ta gargadi wadanda zasu shiga yajin aikin da kada su sake su tare kofofin asibitoci ko kuma kokarin hana mutane shiga asibitoci don a duba lafiyarsu.
A nata bangaren kuma, ta ce za ta tabbata kowanne asibiti na bude, kuma duk ma’aikatan dake son zuwa aiki za’a basu daman shiga wurin aikinsu ba tare da wata matsala ba.
“Shiga yajin aiki a lokacin da ake fama da COVID-19 zagon kasa ne karara, saboda suna ganin gwamnati za ta basu hakuri, kuma ta yi duk abinda suke so, gwamnatinmu ba za ta fifita ma’aikatan kiwon lafiya fiye da sauran ma’aikata ba.
“Wannan shi ne abinda gwamnatocin baya suke yi da ya sa wasu ma’aikata ke ganin sun fi amfani fiye da sauran ma’aikata. Gwamnati ba za ta saduda saboda barazanar yajin aiki ta cire ma’aikatan kiwon lafiya daga cikin ma’aikatan da ta cire ma kashi 25 na albashinsu ba.
“Da kudin muke amfani wajen bayar da tallafi ga mutane gajiyayyu wadanda dokar hana fita ta fi yi ma illa. Sanin kowa ne zaftare albashi ya shafi kowa, tun daga gwamna har karamin ma’aikacin dake amsan abin da yah aura 50,000.” Inji sanarwar.
Sanarwar da ta fito daga mashawarcin gwamna a kan harkar watsa labaru, Muyiwa Adekeye ta bayyana tagomashin da gwamnati ke yi ma’aikatan kiwon lafiya a kowanne rana kamar haka;
1- Ma’aikatan dake aiki kai tsaye da masu cutar COVID-19 na samun alawus N15,000 a rana
2- Ma’aikatan dake daukan samfurin gwaji, sufuri, da bin sawun masu cutar na samun alawus N10,000
3- Sai kuma ma’aikatan dake fuskantar karancin hadari na amsan N5,000.
4- Gwamnati na biyan kafatanin ma’aikatan kiwon lafiya kashi 10 na albashin su.
5- Gwamnati za ta biya N100,000 na tsawon kwanaki 10 ga duk ma’aikacin daya kamu da COVID-19
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng