Gwamnatin Tarayya za ta mayar da yaki da cutar korona a hannun Gwamnoni

Gwamnatin Tarayya za ta mayar da yaki da cutar korona a hannun Gwamnoni

Kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa a kan yaki da cutar korona PTF, ya ce a yayin da zai ci gaba da hadin gwiwa tare da gwamnonin jihohi, ya kuma fara shirin sauya salon daukar mataki na gaba a kan annobar.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, Kwamitin zai dage a kan mayar da akalar yaki da cutar korona a hannu gwamnoni, domin su ci gaba da cin gashin kansu wajen daukar matakai na dakile annobar.

Babban jami'i a kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa, Sani Aliyu, shi ne ya sanar da hakan yayin zaman karin haske tare da sauran 'yan kwamitin a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.

Mista Aliyu ya ce kwamitin zai ci gaba da goyon bayan gwamnonin wajen daukan matakai da zartar da hukunci, tare da yi masu kyakkyawan tanadi na tsare-tsaren da mahukuntan lafiya suka gindaya.

Sai dai ya ce "amma ba za mu ci gaba da daukar wa jihohi matakai ba kai tsaye daga bangaren gwamnatin Tarayya."

Babban jami'i a kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa kan yaki da cutar korona; Sani Aliyu
Babban jami'i a kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa kan yaki da cutar korona; Sani Aliyu
Source: Twitter

KARANTA KUMA: Jihohi 35 da aka samu bullar cutar korona yayin da adadin masu cutar ya kai 7, 016 a Najeriya

"Ya kamata gwamnatocin jihohi su tsaya da kafar su wajen samun ikon aiwatar da matakan da suka dace domin kare lafiya da tseratar da rayukan al'ummar su."

"Saboda haka a wannan batu, daga yanzu gwamnatocin jihohi za su ci gaba da cin gashin kansu da sauke nauyin da ya rataya wuyansu."

"Sai dai kuma muna fata za a samu jituwa da hadin kai a tsakaninmu da gwamnonin wajen amfani da ilimin kimiya tare da la'akari da al'adu na zamantakewa da kuma addinin al'umma yayin daukar matakai."

Ya kara da cewa, "za mu ci gaba da aiki tare da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da duk wani mataki da za a dauka zai kasance ribar da al'umma za ta ci moriya."

A halin yanzu dai adadin mutanen da aka tabbatar cutar korona ta harba a duk fadin Najeriya sun kai 7, 016 kamar yadda alkaluma suka nuna a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel