COVID-19: Ba mu yi fushi ba, za mu sake tura tawagar kwararru Kogi - FG
A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a sake tura tawagar kwararru jihar Kogi don tabbatar da cewa an samar da abubuwan da jihar ke bukata wajen yaki da cutar coronavirus.
Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bada wannan sanarwan a Abuja ga taron manema labarai yayin da suke tattaunawa da kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar shugaban kasa.
Idan za mu tuna, gwamnatin jihar ta hana NCDC bincike ko tallafa mata wajen shirya wa cutar coronavirus a yayin da suka ziyarci jihar.
Wannan zargin ya kawo rashin jituwa tsakanin jami'an NCDC din da jihar Kogi inda jami'an suka bar jihar ba tare da bin dokar gwamna Yahaya Bello ba.
Bayan wannan ci gaban, Ehanire ya ce kwamitin zai tattauna da gwamnan tare da yin aiki da shi don samun hadin kan da zai bai wa NCDC damar yin aikinsu.
Ministan yace ma'aikatar za ta yi aiki tare da jihar don samar da hanyar inganta sadarwa da kuma mika koke.
Ehanire ya ce tawagar bincike da ta sauka jihar Cross River ta dawo kuma ta gano yankunan da ke bukatar kulawa a jihar.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Allah ya yi wa babban dan kasuwar jihar Katsina, Alhaji Danmarke, rasuwa
Ya ce jihar a halin yanzu ta shirya wa ko-ta-kwana.
"Sun kafa kwamiti a kan COVID-19 kuma sun fara samar da takunkumin fuska da kuma kayan kariyar ma'aikatan lafiya," yace.
A wani labari na daban, Uche Achi-Okpaga, sakataren yada labarai na Ohanaeze Ndigbo, ya zargi shugabannin arewa da dora wa yankin kudu nauyin almajiran jihar.
A wata tattaunawar da yayi da jaridar The Punch, Achi-Okpaga ya zargi shugabannin yankin da kirkiro matsala a tsakaninsu ta hanyar mayar da almajiran jihohinsu.
Sau da yawa, kananan yara masu shekaru tsakanin hudu zuwa 15 ake tura su wurin malamai masana ilimin Qur'ani don neman ilimi.
Da yawa daga cikinsu na karewa da bara don samun abinci da sadaka don kuwa malaman basu iya ciyar dasu.
Tun bayan barkewar annobar Coronavirus, wasu gwamnonin a yankin arewa sun dinga mayar da almajirai jihohinsu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng