An sallami ma'aikatan lafiya 40 da su ka kamu da cutar korona a Kano

An sallami ma'aikatan lafiya 40 da su ka kamu da cutar korona a Kano

An sallami arba'in daga cikin ma'aikatan lafiya 50 da su ka kamu da cutar korona a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) bayan sun warke sarai.

Babban darektan asibitin AKTH, Farfesa Abdurrahman Abba Shehe, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin da ya ke karbar tallafin wasu kayan abinci da wani kamfanin magunguna ya bawa asibitin.

"Ba kankanin abin farinciki ba ne a wurinmu cewar ma'aikanmu da su ka kamu da cutar korona a kwanakin baya sun warke. Sakamakon gwajin da aka aiko min ya nuna cewa 40 daga cikinsu sun warke sarai. Babu wanda ya mutu daga cikinsu. An sallamesu ba tare da saka mu su wani sharadi ba," a cewar Farfesa Sheshe.

Ya kara da cewa mutane 10 da ke cibiyar killacewa su na samun sauki sosai kamar yadda rahoton ma'aikatan lafiya a cibiyar killacewa ya nuna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel