Ke duniya: 'Yar shekaru 18 ta kashe mijinta a kan ya bukaci kwanciya da ita

Ke duniya: 'Yar shekaru 18 ta kashe mijinta a kan ya bukaci kwanciya da ita

Wata matar aure mai shekaru 18 mai suna Salma Hassan da ke karamar hukumar Itas Gadau ta jihar Bauchi, ta shiga hannun 'yan sandan jihar sakamakon zarginta da ake da sokawa mijinta wuka.

Ana zargin Salma ta kashe mijinta mai suna Mohammed Mustapha ne a kan auratayya.

Salma, yayin da ta shiga hannun 'yan sandan a hedkwata da ke Bauchi, babban birnin jihar a ranar Alhamis, ta ce ta soka wa mijinta wuka ne saboda ya takurata dole sai ya kwanta da ita a daren.

Ke duniya: 'Yar shekaru 18 ta kashe mijinta a kan ya bukaci kwanciya da ita
Ke duniya: 'Yar shekaru 18 ta kashe mijinta a kan ya bukaci kwanciya da ita Hoto: The Nation
Asali: UGC

Kamar yadda ta bayyana a hedkwatar 'yan sandan, ta ce "Ban so kashe mijina ba, tsautsayi ne. Na soka mishi wuka a kirji ne saboda ya takura ni dole sai ya kwanta dani. Na zata iskanci ne jima'i, shiyasa na ki amince wa.

"Na yi dana-sanin kashe mijina. Na so amfani da wukar ne don tsorata shi. Ban san cewa hakan za ta faru ba," ta kara da cewa.

Salma wacce ta bayyana cewa tana matukar son mijinta, ta ce ta fusata ne don ya ki daina abinda yake nufin yi da ita.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Philip Maku, a yayin zantawa da manema labarai yace Salma ta yi aika-aikar ne a ranar 24 ga watan Afirilun 2020.

Ya ce wani mutum mai suna Haruna Musa ne ya kai rahoton zuwa ofishin 'yan sandan da ke karamar hukumar Itas-Gadau inda daga bisani suka damke ta.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon dan sanda na kin karbar cin hanci a wurin direba ya jawo cece-kuce

Maku yace Mustapha ya ji miyagun raunika kuma an hanzarta kai shi asibiti amma sai aka tabbatar da cewa ya mutu.

A wani labarin kuma, wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Yenagoa, babbar birnin jihar Bayelsa, ta yanke hukunci kan lamarin matashin jihar Kano da ya dauki budurwarsa daga jiharta zuwa Kano.

Kotun ta zargi Yunusa Dahiru wanda aka fi sani da Inusa Yellow da zargin garkuwa da Ese Oruru daga gidansu a Bayelsa zuwa Kano tana yan karamar yarinya sannan ya Musluntar da ita kuma ya aure ta.

Kotun karkashin jagoranicn Alkali Jane Inyang ta yankewa Yunusa Dahiru shekaru 26 a kurkuku kan laifuka biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel