Allah ya yi wa babban dan kasuwar jihar Katsina, Alhaji Danmarke, rasuwa

Allah ya yi wa babban dan kasuwar jihar Katsina, Alhaji Danmarke, rasuwa

Allah ya yi wa shahararren dan kasuwar jihar Katsina, Alhaji Danmarke rasuwa. Sanannen dan kasuwar ya rasu ne a ranar Laraba, 20 ga watan Mayun 2020.

An sallaci gawar dan kasuwar kuma fitaccen dan siyasar jihar Katsinan a yau Alhamis. An birne shi a makabartar Danmarke da ke cikin garin Danmarke a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Danmarke ya rasu yana da shekaru 78 a duniya bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi tare da jinya a wani asibiti mai zaman kansa a Kaduna.

Ustaz Abdulbasir Unguwar Maikawo ne ya jagoranci jana'izar dan kasuwar. Ya yi masa addu'ar yafiyar Allah tare da samun masauki a Aljannar Firdausi.

Danmarke ya rasu ya bar 'ya'ya da yawa da kuma jikoki. Daga ciki kuwa akwai dan takarar kujerar gwamnan jihar Katsina a 2019 karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Danmarke.

Allah ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa tare da jihar Katsina baki daya.

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta yi rashin dakaru 3 sakamakon harin 'yan ta'adda (Hotuna)

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya uku ne suka rasa rayukansu yayin fatattakar 'yan ta'adda, wani jami'i ya sanar.

Shugaban fannin yada labarai na ma'aikatar tsaro, John Enenche, ya bayyana a wata takarda da ta fita a ranar Laraba cewa sojoji uku ne suka rasa rayukansu yayin fatattakar 'yan ta'adda.

Manjo Janar Enenche, ya ce dakarun na daga cikin rundunar Operation Kantana Jimlan wadanda ke sintiri a tsakanin Buni Yadi da Buni Gari na jihar Yobe.

Sun ci karo da abubuwa masu fashewa ne a yayin da suka fatattaki mayakan ta'addancin a ranar Lahadi, jaridar Premium Times.

Ya ce al'amarin ya faru ne a wuri mai nisan kilomita da wani gari da ke karamar hukumar Gujba da ke jihar Yobe yayin da sojoji ukun suka samu raunika sakamakon fashewar bam.

Kamar yadda yace, an kwashesu a motar daukar marasa lafiya amma sai suka sake taka wani abu mai fashewa inda wuta ta kama motar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel