Akwai ganganci a game da kalaman Ministan kwadago – Inji Kungiyar ASUU

Akwai ganganci a game da kalaman Ministan kwadago – Inji Kungiyar ASUU

A ranar Laraba, 20 ga watan Mayu, 2020, kungiyar malaman jami’a, ASUU ta yi wa ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, raddi.

ASUU ta ce kalaman da jami’an gwamnatin su ka yi kwanan nan su na da hadari, kuma ba su dace da su ba. Kungiyar ta maida martani ta bakin shugaban shiyyar Ibadan, Ade Adejumo.

A baya, ministan ya zargi ASUU da zaman gida su na dara yayin da ake kokarin binciko maganin Coronavirus. Ministan ya fadi wannan ne bayan kungiyar ta ki janye aikin da ta ke ta yi.

Farfesa Ade Adejumo ya ce a wuraren da ake aiki da hankali wajen shugabanci, gwamnati za ta rika kokari ne wajen ganin malaman jami’ar gwamnati sun janye yajin aikin da su ke yi.

A cewar shugaban na kungiyar na shiyyar Ibadan, ‘yan ASUU su na bakin kokarinsu na kawo karshen annobar Coronavirus, ko da hakan ya na nufin su yi amfani da kudin aljihunsu.

KU KARANTA: Malaman Jami'a sun tafi yajin aiki

Akwai ganganci a game da kalaman Ministan kwadago – Inji Kungiyar ASUU
Ministan kwadago da Abokan aikinsa. Hoto: Aso Villa
Source: Facebook

Ade Adejumo ya ke cewa malaman jami’a su kan kirkiro na’urorin agazawa numfashi saboda gwamnati ta gaza ware kudi domin bunkasa harkar nazari da bincike a makarantun kasar.

“A wuraren da ake aiki da hankali, mutane irinsu Ngige, murabus za su yi, a kira su tsofaffin ministoci saboda gwamnatinsa ta gagara cika yarjejeniyar da ta shiga da (ASUU).” Inji sa.

A game da zargin da babban akawun gwamnatin Najeriya ya jefi ASUU da ita, kungiyar ta ce ya kamata akawun gwamnatin ya fito ya kare badakalar da ake zargin ana tafkawa ta IPPIS.

Farfesan ya tsaya a kan bakan uwar kungiyar, ya ce tursasawa malamai shiga IPPIS ya sabawa dokar jami’o’i, Sannan ya bukaci AGF ya gayyaci EFCC ta binciki zargin badakalar albashi.

ASUU ta ce annobar COVID-19 ya tonawa gwamnati asiri a Najeriya domin kuwa 8% na kasafin kudin kasar ake warewa harkar ilmi. UNESCO ta kuwa bukaci ilmi ya rika cin akalla 26%.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel