Ganduje ya zaftare kaso 20 zuwa 30 a albashin ma'aikatan jihar Kano

Ganduje ya zaftare kaso 20 zuwa 30 a albashin ma'aikatan jihar Kano

Ma'aikatan gwamnatin jihar Kano da su ka hada da ma'aikatan lafiya da ke yaki da annobar cutar korona sun fara gunaguni bayan karbbar albashinsu na watan Mayu.

Gunagunin ma'aikatan ya biyo bayan zaftare albashinsu da aka yi ba tare da sanin dalili ba, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

A ranar 17 ga watan Mayu ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da zaftare kaso 50 a albashinsa da na sauran zababbu da ma su rike da mukaman siyasa a jihar Kano saboda matsin tattalin arziki da aka shiga sakamakon bullar annobar korona.

Sai dai, gwamnan bai sanar da cewa zai rage albashin ma'aikatan jihar ba.

Jaridar Daily Nigerian ta ce ma'aikatan jihar Kano, wadanda aka fara biya albashin watan Mayu a ranar Laraba, sun gano cewa an yanke kaso 20 zuwa 30 daga cikin albashinsu.

Ganduje ya zaftare kaso 20 zuwa 30 a albashin ma'aikatan jihar Kano
Ganduje ya zaftare kaso 20 zuwa 30 a albashin ma'aikatan jihar Kano. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Kano: Ganduje ya yi wa majami'un jihar feshi, ya saka wa CAN sharadi

Wasu daga cikin ma'aikatan da su ka yi magana da wakilin jaridar Daily Nigerian sun nuna rashin jin dadinsu tare da bayyana hakan a matsayin rashin adalci, musamman a lokacin da ake fama da matsi sakamakon bullar annobar korona wacce ta janyo sanya dokar kulle a jihar.

Wata likita da ke aiki a daya daga cikin asibitan gwamnatin jihar Kano ta ce an zaftare fiye da N30,000, kwatankwacin kaso 21.4, daga albashinta.

"Na yi matukar mamakin ganin an yanke fiye da N30,000 daga cikin albashina. Ragin ya yi yawa, duk da kasancewar tun watan Janairu ake gutsure mana albashi.

"Akwai bukatar gwamnati ta tausaya ma'aikatanta, alabashin nan maleji kawai ake yi da shi saboda yawan bukatu. Ina rokon gwamnati ta janye wannan mataki da ta dauka," a cewarta.

Wani ma'aikaci, wanda mamba ne a kungiyar ma'aikatan Najeriya reshen jihar Kano, ya bayyana rashin jin dadinsa a kan yanke albashin ma'aikata ba tare da wani dalili ba.

A cewarsa, an lalata ma sa lissafin shirin hidimar Sallah da ya ke shirin yi wa iyalinsa saboda an yanke N17,000, kwatankwacin kaso 30, daga albashinsa.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba ta bawa ma'aikatanta wani tallafi ba sakamakon bullar annobar korona, amma a hakan ta yanke shawarar gutsure mu su albashi.

"Abinda ya fi batamin rai shine yadda aka yanke albashin ma'aikata ba tare da sanar da su ba. Wannan rashin adalci ne, ba a yanke shawara ta kirki ba tare da sanarwa ba.

"Gwamna na son yin koyi da gwamnan jihar Kaduna da takwarorinsa na wasu sauran jihohi, hakan ba lallai ya samu karbuwa a nan ba.

"Na gama kasafta yadda zai yi wa iyalina hidima da albashina, amma abin takaici yanzu an rusa min lissafi," a cewarsa.

Da aka tuntubi shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Kano, Kabiru Ado Minjibir, ya ce kungiyarsu ba ta da masaniya a kan yanke albashin ma'aikatan.

Ya kara da cewa kungiyar za ta kira taron ma su ruwa da tsaki domin tattauna yadda za a warware matsalar tare da daukan alkawarin sanar da manema labarai sakamakon tattaunawarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel