Kwamitin Ulama ya nuna rashin amincewa da umarnin Ganduje a kan bude Masallatai a Kano

Kwamitin Ulama ya nuna rashin amincewa da umarnin Ganduje a kan bude Masallatai a Kano

Kwamitin Ulama na manyan malaman addinin Islama a jihar Kano ya nuna hamayyarsa da matakin da gwamna Ganduje ya dauka na bude Coci - Coci da Masallatai domin cigaba da taron ibada.

A ranar Litinin ne gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da cewa za a cigaba da gudanar da Sallar Juma'a a masallatan jihar.

Umarnin na gwamna Ganduje na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Buhari ya tsawaita wa'adin dokar kulle jihar Kano da sati biyu.

A cewar kwamitin Malaman, matakin da Ganduje ya dauka zai haifar da hauhawar wadanda za su kamu da kwayar cutar korona da ke cigaba da yaduwa a jihar, musamman a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Yayin hirarsa da sashen Hausa na radiyon BBC, shugaban kwamitin Ulama na jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce kamata ya yi gwamnati ta fara kallon yadda cutar korona ke yaduwa kafin yanke wannan shawara.

A cewarsa, da gwamnati ta tuntubi kwamitin Ulama na jihar Kano, da za su bayar da shawarar a bawa lafiyar jama'a fifiko.

"Ana fama da wannan annoba, amma, tunda gwamnati ta bar jama'a su cigaba da gudanar da taron ibada, ina shawartar marasa koshin lafiya su kauracewa wuraren taron jama'a. Kazalika, duk mai son kare kansa zai iya kauracewa wuraren ibada.

"Wadanda su ka ga suna son zuwa Masallaci, idan ba su da wata matsala, za su iya zuwa domin yin Sallah a jam'i.

"Babu wani zunubi ga duk wanda ya ki zuwa Masallaci domin yin Sallah a jam'i matukar ya na da dalili mai kwari," a cewar Sheikh Khalil.

Kwamitin Ulama ya nuna rashin amincewa da umarnin Ganduje a kan bude Masallatai a Kano
Sheikh Ibrahim Khalil
Source: Twitter

Gwamna Ganduje ya na cigaba da shan suka a kan matakin da ya dauka na bayar da izinin bude Coci - Coci da Masallatai domin gudanar da ibada.

DUBA WANNAN: Edo da Ondo: APC ta fitar da farashin fom din takarar gwamna da na mataimaki

Sai dai, gwamnan ya ce za a yi amfani da dakarun hukumar Hisbah a Masallatai domin tabbatar da cewa jama'a sun yi biyayya ga matakan kare kai da dakile yaduwar annobar korona a Kano.

Hatta a jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen malamin addini, ya ce bai kamata a bar jama'a su halarci Sallar Eidi a jam'i ba a yayin da ake kokarin dakile yaduwar cutar korona.

Malamin addinin ya bayyana hakan ne yayin da ya ke ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Kaduna bayan kammala taro da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

A cewarsa, Sallar Eidi, wacce ake yi bayan kammala azumin Ramadana, za ta iya bata kokarin gwamnati na shawo kan cutar korona.

Ya ce Najeriya ba kamar kasar Saudiyya ba ce da za a iya sarrafa taron jama'a a wurin ibada ba tare da bayyana cewa cutar za ta yadu cikin sauri ta hanyar sallah a jam'i.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel