Gobarar NIPOST: Pantami ya umarci hukumar da ta bashi gamsasshen rahoto

Gobarar NIPOST: Pantami ya umarci hukumar da ta bashi gamsasshen rahoto

Ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogara da fasahar zamani, Dr Isa Pantami, ya bai wa hukumar NIPOST umarnin bada rahoton gobarar da ta auku a hedkwatarsu a ranar Laraba.

Pantami ya bada wannan umarnin ne a yayin ziyarar da ya kai hedkwatar don duba barnar da gobarar tayi wa ofishin, jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Ya bada umarnin kawo gamsasshen bayani a kan gobarar tare da mika shi zuwa ofishinsa don daukar mataki na gaba.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa Pantami ya samu tarba ne daga shugaban hukumar gaba daya, Isma'il Adewusi, shugabar kwamitin zartarwa ta hukumar, Maimuna Yaya-Abubakar da kuma sauran shugabannin hukumar.

Gobarar NIPOST: Pantami ya umarci hukumar da ta bashi gamsasshen rahoto
Gobarar NIPOST: Pantami ya umarci hukumar da ta bashi gamsasshen rahoto Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Ministan ya nuna farin cikinsa ta yadda aka shawo kan gobarar da gaggawa.

"Muna godiya ga Allah ta yadda aka dakile wutar da wuri tare da hana ta kaiwa sauran ofisohin da ke hedkwatar. Ba ta lalata muhimman takardun hukumar ba," yace.

KU KARANTA KUMA: Sallar idi: An samu sabani tsakanin sarkin Musulmi da wasu gwamnonin arewa

Tun farko, Adewusi ya sanar da ministan cewa rahoton hukumar kashe gobara ta tarayya wanda a lokacin suke jira shine zai bayyana tushen gobarar.

A baya mun ji cewa mumunar gobara ya auku a hedkwatar hukumar ayyukan aika da karban sako watau NIPOST dake birnin tarayya Abuja.

Rahoton TheCable ya bayyana cewa gobarar ta fara ci ne tun karfe 9 na safiyar ranar Laraba, 20 ga May, 2020.

An samu labarin cewa ma'aikata da yawa na cikin ofishin lokacin da wutar ta fara ci amma daga baya jami'an kwana-kwana sun samu nasarar kashe wutar.

Wannan shine karo na biyar da manyan ofishohin gwamnatin tarayya a Abuja ke gobara duk da cewa maaikata na zaune a gidajensu.

An umurci ma'aikatan gwamnati suyi zamansu a gida saboda dokar ta bacin da gwamnatin tarayya ta sanya a Abuja.

Idan baku manta ba, a ranar 21 ga Afrilu, anyi gobara a ofishin babban bankin Najeriya CBN, reshen Jos, jihar Plateau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel