Ke duniya, ina zaki da mu? Kalli yadda ake hada hadar cinikin sassan mutum a Ogun
Allah Ya tona asirin wasu miyagun mutane masu cinikin sassan jikin dan Adam bayan wani rikici ya barke a tsakaninsu, wanda hakan tasa a kan tsince su a rana tsamo tsamo.
Punch ta ruwaito rikicin ya samo asali ne bayan masu sayar da sassan sun farauto sun kawo, amma masu saye sun gaza biyan kudin da suka yi alkawari za su saya a kai, naira miliyan 1.
KU KARANTA: Yaki da yan bindiga: Dakarun hadaka sun isa jahar Katsina don gudanar da aiki na musamman
Hakan ya harzuka su, inda suka tafi dasu cikin daji a jahar Ogun, a nan suka ce da wa Allah Ya hada mu idan ku ba, suka lakada musu dan banzan duka a bakacin wahalan da suka yi.
Rahotanni sun bayyana wasu mutane uku ne suka tuntubi masu sayar da sassan jikin mutum a Ogun, inda suka nemi su kawo musu hannun mutum domin a musu tsafin samun kudi.
Masu neman hannun sun hada da Mathew Idosu, John Feyisetan da Samuel Adegbola sun yi yarjejeniya da masu kawo musu hannun a kan za su sayi hannun a kan kudi naira miliyan 1.
Kakaakin Yansandan jahar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace sun kama mutanen uku da wani boka Michael Itomu da hadin gwiwar yan bangan jahar.
“A Idi-iroko cikin karamar hukumar Ipokia muka kama su dauke da hannun dan Adam, amma da aka kawo musu hannun, sai suka gagara biyan kudin, hakan ya janyo rikici a tsakaninsu, daga nan masu hannun suka dauke Samuel da John zuwa wani daji, suka casa su kafin su sake su a ranar 17 ga wata.
“Wannan lamari ne ya tona asirinsu har aka gane harkar da suke yi. A yanzu haka mun ajiye hannun a babban asibitin Idi-Iroko, kuma an mika maganan zuwa sashin binciken manyan laifuka don kammala bincike.” Inji shi.
Daga karshe Oyeyemi yace kwamishinan Yansandan jahar, Kenneth Ebrimson ya bada umarnin farauto wadanda suka sayar da sassan jikin a duk inda suke don su fuskancin hukunci.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng