Buhari ya sallami shugaban NECO da manyan jami'an hukumar 4

Buhari ya sallami shugaban NECO da manyan jami'an hukumar 4

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kori shugaban hukumar tsara jarrabawar kammala makarantar sakandire (NECO), Charles Uwake, da sauran wasu jami'an hukumar hudu a kan wasu laifuka ma su nasaba da almundahana.

Korarar ma'aikatan ta biyo bayan shawarar rahoton kwamitin bincike da aka kafa, wanda a farko ya bayar da shawarar dakatar da su.

A wata takarda mai dauke da sa hannun babban sakataren hukumar NECO, Sonny Echono, an zargi Uwake da saba dokokin gwamnati na bayar da kwangila.

A cikin wani jawabi da Azeez Sani, shugaban sashen yada labarai na NECO, ya ce, "shugaban kasa, bisa dogaro da ikon da kundin tsarin mulki ya bashi, ya amince da sallamar shugaban NECO da aka dakatar."

An umarce shi ya mika sauran takardu da kayan gwamnati da ke hannunsa zuwa ga mukaddashin shugaban hukumar.

Sauran manyan jami'an hukumar da aka kora tare da shugaban sune; Mista Bamidele Olure (darektan kudi da asusu), Dakta Shina Adetona (shugaban sashen harkokin kwangila), Mista Tayo Odukoya (mataimakin darekta) da Barista Babatunde Aina (shugaban bangaren shari'a).

Buhari ya sallami shugaban NECO da manyan jami'an hukumar 4
Charles Uwake
Source: UGC

An kori Olure, darektan kudi da asusu, saboda almundahanar kudi da rashin dacewa wajen shugabantar bangaren kudi.

DUBA WANNAN: Kun yi ma na aringizo - Gwamnatin Zamfara ta musanta NDDC a kan alkaluman ma su korona

Kazalika, an kori Adetona, shugaban bangaren kwangila, bayan samunsa da laifuka ma su nasaba da barna da take ka'idojin aiki.

Odukoya, mataimakin darekta, ya rasa aikinsa ne saboda karya dokokin aiki.

An kori Aina, shugaban bangaren shari'a, daga aiki bayan samunsa da laifin aikata karya, rashin gaskiya yayin gudanar da aiki da kuma sayar da gidan hutawar ma'aikatan NECO, laifin da EFCC ke bincikarsa a kai.

Wasikar ta bukaci hukumar NECO ta fara daukan matakai da bin hanyoyin kwato dukkan kadarori da wata dukiya da Odukoya ya samu ta hanyar amfani da wani kamfaninsa mai suna M/S I-Web.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel