COVID-19: Sai mun kawo karshen dukkan damuwar Kanawa - Ganduje

COVID-19: Sai mun kawo karshen dukkan damuwar Kanawa - Ganduje

A jiya Laraba ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da jama'ar jihar cewa yana yin duk abinda ya dace don dawo musu da kwanciyar hankalinsu.

Ganduje ya ce gwamnatinsa tana sane da matsalolin da jama'ar jihar ke ciki kuma yana kokarin shawo kan matsalolin.

Yace daga cikin dalilin sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar da kara kwana daya na walwala shine don a bar mutane su ci gaba da walwalarsu tare da kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar.

COVID-19: Sai mun kawo karshen dukkan damuwar Kanawa - Ganduje
COVID-19: Sai mun kawo karshen dukkan damuwar Kanawa - Ganduje Hoto: Daily Nigerian
Source: Twitter

"Gwamnati ta bada fifiko wajen kiyayewa tare da bada kariya ga rayukan jama'a. Hakan yasa ta takaita dokar hana zirga-zirga," gwamnan ya kara da cewa.

A yayin jawabi ga malaman addini da yayi taro dasu, Gwamnan Ganduje ya yi kira garesu da su fahimci annobar kuma su gane cewa dokokin da aka saka ba na dindindin bane, na wucin-gadi ne don bada kariya ga rayuka.

"Akwai manyan matakan da aka dauka don dakile yaduwar cutar kuma ta wannan hanyoyin ne kadai za a iya tseratar da rayukan.

"Amma kuma mun bada ranakun bude harkokin jihar don bai wa jama'a damar neman kudi da yin bauta.

"Ranakun Laraba, Juma'a da Lahadi ne muka amince amma dole a kiyaye dokokin dakile yaduwar muguwar cutar da suka hada da saka takunkumin fuska, wanke hannu da kuma amfani da sinadarin tsaftace hannu," Ganduje yace.

A gefe guda, gwamnatin jihar Kano ta yi wa majami'u 31 na jihar feshin hana yaduwar cutar coronavirus, Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana.

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin taron da yayi da kungiyar mabiya addinin Kirista ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kano a gidan gwamnatin jihar.

Kamar yadda yace, hadin kan mabiya addinin Kiristan da masu ruwa da tsaki ya zama dole wajen shawo kan annobar a jihar.

Gwamnan ya yi kira ga shugabannin da sauran mazauna jihar da su kiyaye dokokin masana kiwon lafiya, jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel