Coronavirus: Gwamnatin Amurka ta baiwa Najeriya taimakon dala miliyan 33

Coronavirus: Gwamnatin Amurka ta baiwa Najeriya taimakon dala miliyan 33

Gwamnatin kasar Amurka ta baiwa Najeriya kyautar zambar kudi $33m, kimanin naira biliyan 12.89 kenan a matsayin tallafin yaki da annobar Coronavirus a kasar.

Punch ta ruwaito jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard ce ta bayyana haka a ranar Laraba yayin hira da ta yi a wani gidan rediyo Lagos Talk 91.3FM.

KU KARANTA: Duk da matsalar Corona, likitoci sun shiga yajin aikin dindindin a Najeriya

Mary ta ce zuwa yanzu Amurka ta tallafa ma kasashen duniya da dama da kudi dala biliyan 2, duk a kokarinta na ganin an hada karfi da karfe wajen shawo kan cutar.

Haka zalika ta kara da cewa Amurka da Najeriya na cigaba da tattaunawa a tsakaninsu domin fadada hanyoyin da za su bi wajen yaki da cutar.

Coronavirus: Gwamnatun Amurka ta baiwa Najeriya taimakon dala miliyan 33
Buhari da Mary Hoto: Pulse
Source: UGC

“Mun baiwa Najeriya dala miliyan 33 don yaki da COVID-19, muna kuma lalubo hanyoyin da za mu bi don hadin gwiwa da juna, muna kuma lura da yadda ake kula da marasa lafiya a kasashen biyu.

“Tabbas muna aiki tare sosai a wannan lokaci, sama da shekaru 20 kenan Amurka na taimaka ma Najeriya ta bangaren kiwon lafiya, kamfanonin Amurka da dama suna taimakawa a Najeriya don yaki da cutar.” Inji ta.

A tuna a ranar 28 ga watan Afrilu ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi magana da shugaba Muhammadu Buhari ta wayar tarho, inda ya yi alkawarin taimaka ma Najeriya.

Shugaban Amurkan ne ya kira Buhari, inda ya shaida masa cewa za su aiko ma Najeriya na’aurar taimaka ma numfashi watau Ventilators domin kulawa da masu cutar Coronavirus.

A wani labarin kuma, Kungiyar likitocin Najeriya, reshen jahar Legas ta umarci yayanta su fara yajin aikin sai yajin aikin sai ‘baba ta ji’ daga karshe 6 na yammacin Laraba, 20 ga watan Mayu.

Likitocin sun dauki wannan mataki ne biyo bayan cin zarafin su da jami’an Yansanda suke yi a kan hanya, musamman yayin da suke tafiya wajen aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel