Akwai yiwuwar muyi karin kuɗin biredi - Kungiya

Akwai yiwuwar muyi karin kuɗin biredi - Kungiya

Masu gidajen biredi na jihar Legas sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta shiga lamarinsu a kan yadda kayayyakin aikinsu ke tashi. Hakan zai iya shafar farashin biredin da karin kashi 60 a nan kusa.

Masu gidajen biredin sun koka a kan cewa kayayyakin sun tashi ne sakamakon annobar COVID-19 da ta zama ruwan dare, jaridar The Nation ta wallafa.

A wata takarda da shugabannin kungiyoyin na jihar Legas, Kwamared Taiwo Akintola da Kwamared Ibitoye Oladapo suka saka hannu, kungiyoyin sun nuna damuwarsu matuka a kan halin da suke ciki.

Kamar yadda kungiyar ta bayyana, tashin farashin kayan na iya kashe kasuwancinsu domin suna matukar shan wahala wajen fitar da riba.

"Buhun fulawa da ke N9,000 kafin COVID-19 yanzu N13,000. Buhun sukari kuwa da ke N13,000 a da yanzu ya kai N24,000.

"Bota a halin yanzu N12,000 ne a maimakon N7,500. Madara a da N29,000 take amma a yanzu N52,000," kungiyar tace.

Akwai yuwuwar hauhawar farashin biredi da 60% - Kungiya
Akwai yuwuwar hauhawar farashin biredi da 60% - Kungiya. Hoto daga Getty Images
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: FG ta tsige shugaban TCN

Sun kara da cewa farashin yis da sauran sinadaran da ake zubawa biredin duk ya yi tashin gwauron zabi.

Kungiyar ta yi bayanin cewa rashin daidaituwa a bangaren canji, farashin man fetur da sauran kayayyaki na daga cikin dalilan da suke kawo tashin farashin fulawa.

Kungiyar ta yi kira ga masu kamfanonin fulawa da sauran kayayyakin hadin biredin da su sassauta farashin amma har yanzu shiru.

"A saboda haka ne muke mika kokon barar mu ga gwamnatin tarayya da ta saka hannu a al'amarin don farashin kayayyaki su sauka kasa.

"Kungiyar Master Bakers na daya daga cikin manyan gidajen biredin da ke kasar nan amma kuma ahalin yanzu suna ta karyewa. Wadanda suka rasa ayyukansu suna da tarin yawa," kungiyar ta kara da cewa.

A yayin kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su gaggauta shigowa cikin lamarin don amfanin kowa.

"Idan kayayyaki suka ci gaba da tashin da suke yi yanzu, akwai yuwuwar farashin biredi ya karu da kashi 60," kungiyar tace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel