Duk da matsalar Corona, likitoci sun shiga yajin aikin dindindin a Najeriya

Duk da matsalar Corona, likitoci sun shiga yajin aikin dindindin a Najeriya

Kungiyar likitocin Najeriya, NMA, reshen jahar Legas ta umarci yayanta su fara yajin aikin sai yajin aikin sai ‘baba ta ji’ daga karshe 6 na yammacin Laraba, 20 ga watan Mayu.

Daily Trust ta ruwaito likitocin sun dauki wannan mataki ne biyo bayan cin zarafin su da jami’an Yansanda suke yi a kan hanya, musamman yayin da suke tafiya wajen aiki.

KU KARANTA: Coronavirus: Hukumar gwamnatin tarayya ta zaftare kashi 50 na albashin ma’aikatanta

Shugaban kungiyar, Saliu Oseni ne da sakatarensa Ramon Moronkola ne suka sanar da haka cikin wata sanarwa da suka fitar inda suka ce:

“Duk wani likita dake karkashin kungiyar NMA reshen jahar Legas ya fara yajin aiki na dindindin daga karfe 6 na ranar Laraba, har sai lokacin da gwamnatin jahar Legas tare da kwamishinan Yansandan jahar Hakeem Odumosu suka lalubo hanyar daya kamata su bi don dabbaka umarnin zaman gida.

“Musamman dangane da tsarin baiwa ma’aikata na musamman daman fita don gudanar da aikinsu, wanda suka hada da likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya.” Inji shi.

Duk da matsalar Corona, likitoci sun shiga yajin aikin dindindin a Najeriya

Likitoci Hoto: TVC
Source: UGC

Kazalika NMA ta bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su bata takarda a rubuce dake tabbatar da matsayin likitoci a matsayin masu gudanar da muhimmin aiki a wannan lokaci.

“Kuma a tallata wannan takarda a shafukan sadarwar zamani da gidajen rediyo da na jaridu, sa’annan a kawo mana kwafin takardar zuwa sakatariyar hukumar NMA reshen jahar Legas don ya zama hujja.”

Wannan rikici ya biyo bayan wuce gona da iri da jami’an tsaro suke yi ne a aikinsu a kokarinsu na dabbaka umarnin shugaban kasa na hana zirga zirga daga karfe 6 na safe zuwa 8 na dare.

Da wannan ne jami’an tsaro suka kama jami’an kiwon lafiya da yan jaridu da dama, amma daga bisani an sake su bayan manyan jami’an Yansanda daga Abuja sun sa baki.

Sai dai ta danganta cin zarafin nan ga samun sabani a umarnin da gwamnatin tarayya da gwamnatin jahar Legas suke bayarwa, wanda hakan yasa aka rasa wanne ne ba wanne ne ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel