Garkame mutane a gida ya iya fin ciwon Coronavirus hadari – Jami'in UNICEF

Garkame mutane a gida ya iya fin ciwon Coronavirus hadari – Jami'in UNICEF

Hukumar UNICEF ta ja-kunne cewa rufe mutane da ake yi a gida a hana su fita ya na iya yin barnar da ta fi ta ainihin cutar COVID-19 a wasu kasashe.

UNICEF ta na hasashen akalla kananan yara miliyan 1.2 za su mutu a fadin Duniya a sanadiyyar zaman gida da za a tursasa mutane a wasu kananan kasashe.

Wannan gargadi na UNICEF ya zo daidai lokacin da wasu likitocin duniya su ke bada shawarar gwamnatoci da shugabanni su daina sa kudi a asusun WHO.

A cewar UNICEF, rufe mutane a gida ba zai yi maganin annobar ba. Gargadin ya zo ne yayin da ake shirin fara wani taron kasashe na harkar kiwon lafiya.

Tursasawa mutane zaman kulle ba hanya ba ce ta yaki da cutar COVID-19, kuma zaman gidan zai taimaka wajen karuwar mutuwar kananan yara da kashi 45%.

KU KARANTA: Najeriya ta shiga cikin kasashe 5 da ake fama da Coronavirus a Afrika

Ta ce hadarin da kananan yara za su shiga na kamuwa da masassara, ciwon sanyi da gudawa a kasashe masu tasowa saboda zaman gida ya zarce illar cutar.

Babban likitan UNICEF, Dr Stefan Peterson ya fadawa jaridar Telegraph cewa: “Hana mutane fita bai da wani tasirin a-zo-a-gani wajen maganin Coronavirus."

“Idan ka fadawa mutanen da ke zaune a wuraren da babu ruwa da abinci su zauna a cikin dakinsu, wannan ba zai takaita yaduwar cutar ba.” Inji Stefan Peterson

“Kasashen da ba su san abin da za su yi ba, sun kinkimo tsarin takunkumin daga wasu wurare, ba tare da sun duba yadda za su yi la’akari da matsalolinsu ba.”

Kwararen masanin na UNICEF ya ce kowace mace za ta yi kitso ne daidai gashinta, don haka ya yi kira ga kasashe su nemi irin dabarar da za ta ceci mutanensu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel