Matar mataimakin marigayi janar Sani Abacha ta rasu

Matar mataimakin marigayi janar Sani Abacha ta rasu

Cif Deborah Folashade Diya, matar tsohon shugaban rundunar sojoji, laftanal janar Oladipo Diya (mai ritaya), ta mutu.

Femi Adesina, kakakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatar da mutuwarta a cikin sakon ta'aziyyar da ya fitar a ranar Laraba.

Adesina ya ce shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan tsohon shugaban rundunar sojin tare da yin addu'ar Allah ya ba su hakurin jure rashin da su ka yi.

Ya kara da cewa shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya ji kan marigayiyar.

"Shugaban kasa ya shiga sahun jerin sahun abokai, musamman mambobin kungiyar Cocin 'United African Methodist (Evangelical), wajen mika sakon ta'aziyyar rashin Cif Folashade Diya, wacce ta sadaukar da rayuwarta wajen bautar Ubangiji da kyautatawa jama'a'', a cewarsa.

Buhari ya ce marigayiyar ta zama abin koyi a wurin mutane da dama, musamman a bangaren nuna kaunar jama'a, tsoron Allah, da halaye na gari.

Laftanal Janar Diya ya kasance mataimaki ga tsohon shugaban kasa, marigayi janar Sani Abacha, daga shekarar 1994 zuwa shekarar 1997, lokacin da aka kama shi bisa zargin laifin cin amana.

Matar mataimakin marigayi janar Sani Abacha ta rasu

Folashade Diya; Matar mataimakin marigayi janar Sani Abacha
Source: UGC

Da yammacin ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa labarin cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Sheikh Ahmed Lemu na rasuwar babbar dansa, Abubakar Shehu Lemu.

A cikin jawabin da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar ranar Talata, shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga ilahirin mutanen jihar Neja bisa rashin da ya kira da 'wanda ba za a maye gurbinsa ba'.

DUBA WANNAN: Zargin cin amana: 'Yan sanda sun bazama neman magidancin da ya like al'aurar matarsa da 'sufagilu'

A cikin sakon, Buhari ya ce, amadadinsa tare da iyalinsa, ya na taya Sheikh Lemu jimamin rashin da ya yi.

"Na san tilas za ka kasance cikin radadin rashin babban yaronka," kamar yadda ya kara da cewa.

Ya roki Allah ya bawa Sheikh Lemu da iyalinsa hakurin jure rashin da ya samesu tare da rokawa mamacin rahamar Ubangiji.

Marigayi Abubakar, darekta a ma'aikatar harkokin kasashen waje, ya mutu bayan ya sha fama da doguwar jinya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel